Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Yesu ya sāke yin musu magana da misalai, yana cewa,

  2. Sai Farisiyawa suka yi waje, suka ƙulla yadda za su yi masa tarko cikin maganarsa.

  3. Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba.

  4. To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?”

  5. Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?

  6. Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari,

  7. sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?”

  8. Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”

  9. Da suka ji haka, sai suka yi mamaki. Saboda haka suka ƙyale shi, suka yi tafiyarsu.

  10. A ranan nan Sadukiyawa, waɗanda suke cewa babu tashin matattu, suka zo wurinsa da tambaya.

  11. Yesu ya amsa ya ce, “Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba.

  12. Da taro suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.

  13. Da jin Yesu ya ƙure Sadukiyawa, sai Farisiyawa suka tattaru.

  14. Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya.

  15. Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’

  16. Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su,

  17. “Me kuke tsammani game da Kiristi? Ɗan wane ne shi?” Suka amsa suka ce, “Ɗan Dawuda.”

  18. Ya ce musu, “To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce,

  19. “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’

  20. To, in Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji,’ yaya zai zama ɗansa?”

  21. Ba wanda ya iya tanka masa, daga wannan rana kuwa ba wanda ya sāke yin karambanin yin masa wata tambaya.

  22. Sa’an nan Yesu ya ce wa taron mutane da kuma almajiransa,

  23. “Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ’yan’uwa ne.

  24. Kada kuma ku kira wani a duniya ‘uba,’ gama kuna da Uba ɗaya ne, yana kuwa a sama.

  25. Ba kuwa za a kira ku ‘malam’ ba, gama kuna da Malami ɗaya ne, Kiristi.