Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Saurayin ya ce, “Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?”

  2. Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”

  3. Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki yă shiga mulkin sama.

  4. Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”

  5. Sa’ad da almajiran suka ji wannan, sai suka yi mamaki ƙwarai. Suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai sami ceto ke nan?”

  6. Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne.”

  7. Sai Bitrus ya amsa masa, “Ga shi mun bar kome don mu bi ka! Me za mu samu ke nan?”

  8. Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, a lokacin sabunta dukan kome, sa’ad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai daraja, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.

  9. Duk kuma wanda ya bar gidaje ko ’yan’uwa maza ko ’yan’uwa mata ko mahaifi ko mahaifiya ko yara ko gonaki, saboda ni, zai sami abin da ya fi haka riɓi ɗari, yă kuma gāji rai madawwami.

  10. To, da Yesu yana haurawa zuwa Urushalima, sai ya ja almajiran nan goma sha biyu gefe, ya ce musu,

  11. “Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa

  12. za su kuma bashe shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!”

  13. Sai mahaifiyar ’ya’yan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ’ya’yanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yă yi mata wani abu.

  14. Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?” Ta ce, “Ka sa daga cikin ’ya’yan nan nawa biyu, ɗaya yă zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.”

  15. Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?” Suka amsa, “Za mu iya.”

  16. Yesu ya ce musu, “Tabbatacce za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.”

  17. Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko.

  18. kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

  19. Sa’ad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi.

  20. Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

  21. Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

  22. Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”

  23. Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.”

  24. Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.

  25. Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu,