Skip to content

Joses

5 ayoyi · 6 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Joses

  1. Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu, ’yan’uwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba?

  2. A cikinsu, akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu uwar Yaƙub da Yoses, da kuma uwar ’ya’yan Zebedi.

  3. Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.

  4. Waɗansu mata suna kallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yusuf, da kuma Salome.

  5. Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi.