Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. “An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’

  2. “Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’

  3. “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.

  4. Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’

  5. “Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’

  6. “Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba.

  7. “Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama.

  8. Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki.

  9. Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa.

  10. “Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya.

  11. Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni,

  12. da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’

  13. “Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha?

  14. Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura?

  15. Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’

  16. “Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’

  17. “Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa.

  18. Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba,

  19. da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’

  20. “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’

  21. “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’

  22. Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa,

  23. “Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.”

  24. suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.

  25. Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu,