Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Amma mutumin Allah ya zo wurinsa ya ce, “Ya sarki, waɗannan runduna daga Isra’ila ba za su tafi tare da kai ba, gama Ubangiji ba ya tare da Isra’ila, ba ya nan da wani cikin mutanen Efraim.

  2. Ko da ma ya tafi ya yi faɗa da ƙwazo a cikin yaƙi, Allah zai tumɓuke shi a gaban abokan gāba, gama Allah yana da iko yă taimaka ko yă tumɓuke.”

  3. Amaziya ya tambayi mutumin Allah ya ce, “Amma game da talenti ɗarin da na biya saboda waɗannan rundunonin Isra’ila fa?” Mutumin Allah ya amsa, “Ubangiji zai ba ka fiye da wannan.”

  4. Fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan Amaziya, sai ya aiki wani annabi wurinsa wanda ya ce, “Me ya sa ka nemi shawarar allolin mutanen nan, waɗanda ba za su cece mutanensu daga hannunka ba?”

  5. Tun yana cikin magana, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Rufe mana baki! Me zai hana a kashe ka?” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”

  6. Amma Amaziya bai saurara ba gama Allah ya yi haka domin yă miƙa su ga Yehowash, domin sun nemi shawarar allolin Edom.

  7. Ya kwashe dukan zinariya da azurfa da dukan kayayyakin da aka samu a haikalin Allah waɗanda suke a ƙarƙashin kulawar Obed-Edom, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya.

  8. Sa’ad da Amaziya ya bar bin Ubangiji, aka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma suka aiki mutane suka bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi.

  9. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar dai yadda mahaifinsa Amaziya ya yi.

  10. Ya nemi Allah a kwanakin Zakariya, wanda ya koyar da shi a tsoron Allah. Muddin ya nemi Ubangiji, Allah ya ba shi nasara.

  11. Allah ya taimake shi a kan Filistiyawa da kuma a kan Larabawa waɗanda suke zama a Gur-Ba’al da kuma a kan Meyunawa.

  12. Amma bayan Uzziya ya zama mai iko, sai ɗaga kai ya kai shi ga fāɗuwa. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa ba, ya kuma shiga haikalin Ubangiji don yă ƙone turare a bagaden turare.

  13. Azariya firist tare da waɗansu firistoci tamanin na Ubangiji masu ƙarfin hali suka bi shi ciki.

  14. Suka kalubalance shi suka ce, “Ba daidai ba ne, Uzziya, ka ƙone turare ga Ubangiji. Wannan aikin firistoci zuriyar Haruna ne, waɗanda aka tsarkake don ƙone turare. Ka bar wuri mai tsarki, gama ka kasance marar aminci; kuma Ubangiji Allah ba zai girmama ka ba.”

  15. Uzziya wanda yake da farantin wuta a hannunsa a shirye don ƙone turare, ya husata. Yayinda yake fushi da firistocin a gabansu a gaban bagaden turare a haikalin Ubangiji, sai kuturta ta faso a goshinsa.

  16. Sa’ad da Azariya babban firist da dukan sauran firistoci suka dube shi, sai suka ga cewa yana da kuturta a goshinsa, saboda haka suka gaggauta tunkuɗa shi waje nan da nan. Tabbatacce, shi kansa ma ya yi marmari yă bar wurin domin Ubangiji ya buge shi.

  17. Sarki Uzziya ya kasance da kuturta har ranar mutuwarsa. Ya zauna a gidan da aka ware, da kuturci, aka kuma ware shi daga haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa ya lura da fadan ya kuma yi mulkin mutanen ƙasar.

  18. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda mahaifinsa Uzziya ya yi, sai dai bai kutsa cikin haikalin Ubangiji kamar mahaifinsa ba. Mutane kuwa, suka ci gaba da aikata ayyukan lalaci.

  19. Yotam ya sāke ginin Ƙofar Bisa na haikalin Ubangiji, ya kuma yi aiki sosai a katanga a tudun Ofel.

  20. Yotam ya ƙaru a iko saboda ya daidaita al’amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa.

  21. Ahaz yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Ba kamar Dawuda kakansa ba, bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji ba.

  22. Ya ƙone hadayu a Kwarin Ben Hinnom, ya kuma miƙa ’ya’yansa maza a cikin wuta, yana bin hanyoyi banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.

  23. Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya miƙa shi ga sarkin Aram. Arameyawa suka ci shi a yaƙi, suka kuma kwashe mutanensa da yawa a matsayin ’yan kurkuku, suka kawo Damaskus. Ya kuma ba da shi ga sarkin Isra’ila, wanda ya jijji masa a yaƙi.

  24. A rana ɗaya Feka ɗan Remaliya ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu ashirin a Yahuda, domin Yahuda sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu.

  25. Amma wani annabin Ubangiji mai suna Oded yana a can, sai ya fito don yă sadu da mayaƙa sa’ad da suke komowa zuwa Samariya. Ya ce musu, “Domin Ubangiji Allah na kakanninku yana fushi da Yahuda, ya ba da su cikin hannunku. Sai kuka kashe su cikin fushin da ya kai sama.