Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. A rana ta huɗu sai suka taru a Kwarin Beraka, inda suka yabi Ubangiji. Wannan ne ya sa ake kiransa Kwarin Beraka har wa yau.

  2. Sa’an nan Yehoshafat ya jagoranci dukan mutanen Yahuda da Urushalima suka dawo da farin ciki zuwa Urushalima, gama Ubangiji ya ba su dalilin farin ciki a kan abokan gābansu.

  3. Suka shiga Urushalima suka shiga haikalin Ubangiji da kiɗin molaye da sarewa da kuma garayu.

  4. Tsoron Allah ya kama dukan mulkokin ƙasashe sa’ad da suka ji yadda Ubangiji ya yi yaƙi a kan abokan gāban Isra’ila.

  5. Mulkin Yehoshafat kuwa ya zauna lafiya, gama Allahnsa ya ba shi hutu a kowane gefe.

  6. Ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa bai kuwa kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji.

  7. Duk da haka ba a kawar da masujadai kan tudu ba, domin har yanzu mutanen ba su tsayar da zukatansu ga Allahn kakanninsu ba.

  8. Eliyezer ɗan Dodabahu na Maresha ya yi annabci a kan Yehoshafat cewa, “Domin ka haɗa kai da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Jiragen ruwan kuwa suka farfashe, ba a kuwa iya sa su je kasuwanci ba.

  9. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, kamar yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri ’yar Ahab. Ya aikata mugayen ayyuka a idon Ubangiji.

  10. Duk da haka, domin alkawarin da Ubangiji ya yi wa Dawuda, Ubangiji bai so yă hallaka gidan Dawuda ba. Ubangiji ya riga ya yi alkawari zai ci gaba da riƙe fitila domin Dawuda da zuriyarsa har abada.

  11. Har yă zuwa yau Edom na tawaye a kan Yahuda. Libna ya yi tawaye a lokaci guda, domin Yehoram ya yashe Ubangiji Allah na kakanninsa.

  12. Yehoram ya sami wasiƙa daga Iliya annabi, wadda ta ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda ya ce, ‘Ba ka yi tafiya a hanyoyin mahaifinka Yehoshafat ko Asa sarkin Yahuda ba.

  13. Saboda haka a yanzu Ubangiji yana shirin ya bugi mutanenka, ’ya’yanka maza, matanka da kuma kome da yake naka, da bugu mai ƙarfi.

  14. Ubangiji ya sa Filistiyawa da Larabawa waɗanda suke zama kusa da Kushawa su yi gāba da Yehoram

  15. Bayan dukan wannan, sai Ubangiji ya sa wa Yehoram cuta marar warkarwa ta ciki.

  16. Ya aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, yadda gidan Ahab ta yi, gama bayan mutuwar mahaifinsa, sai gidan Ahab ta zama masu ba shi shawara, shawarar da ta kai shi ga lalacewa.

  17. Ta wurin ziyarar Yoram, Allah ya kawo fāɗuwar Ahaziya. Sa’ad da Ahaziya ya iso, ya tafi tare da Yoram domin yă sadu da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya shafe don yă hallaka gidan Ahab.

  18. Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa’ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama sun ce, “Shi jikan Yehoshafat ne, wanda ya nemi Ubangiji da dukan zuciyarsa.” Ta haka babu wani a gidan Ahaziya da yake da ƙarfin cin gaba da mulkin.

  19. Ya kasance a ɓoye tare da su a haikalin Allah shekara shida, yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.

  20. dukan taron suka yi alkawari da sarki a haikalin Allah. Yehohiyada ya ce musu, “Ɗan sarki zai yi mulki yadda Ubangiji ya yi alkawari game da zuriyar Dawuda.

  21. kashi ɗaya bisa ukunku a fadan sarki, kashi ɗaya bisa uku kuma, a Ƙofar Harsashi, sai kuma dukan sauran mutane su kasance a filayen haikalin Ubangiji.

  22. Babu wanda zai shiga haikalin Ubangiji sai firistoci da Lawiyawan da suke a aiki; za su iya shiga domin su tsarkaku ne, amma sauran mutane za su kiyaye abin da Ubangiji ya sa su yi.

  23. Sa’an nan ya ba shugabannin māsu da garkuwoyi manya da ƙanana na sarki Dawuda, waɗanda suke cikin haikalin Allah.

  24. Yehohiyada da ’ya’yansa maza suka fitar da ɗan sarki suka sa rawani a kansa; suka miƙa masa alkawarin, suka kuma yi shelarsa a matsayin sarki. Suka shafe shi suka kuma tā da murya suna cewa, “Ran sarki yă daɗe!”

  25. Sa’ad da Ataliya ta ji surutun mutane suna gudu suna yabon sarki, sai ta tafi wurinsu a haikalin Ubangiji.