God
Ayoyin da suka ambaci God
Ya faɗa musu, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari’ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa’ad da kuke yanke shari’a.
Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci.”
A Urushalima kuma, Yehoshafat ya naɗa waɗansu Lawiyawa, firistoci da kawunan iyalan Isra’ilawa don su tabbatar da an bi dokar Ubangiji, su kuma sasanta tsakanin mutane. A Urushalima za su zauna.
Ya ba su waɗannan umarnai, “Ku yi aikinku da aminci da tsoron Ubangiji da dukan zuciyarku.
Cikin kowane batun da ya zo gabanku daga ’yan’uwanku waɗanda suke zama a birane, ko batun na kisa ne ko kuwa waɗansu batuttuwan da suka shafi doka, umarnai, ƙa’idodi ko farillai, dole ku ja musu kunne kada su yi wa Ubangiji zunubi; in ba haka ba fushinsa zai sauko a kanku da ’yan’uwanku. Ku yi wannan, ta haka ba za ku kuwa yi zunubi ba.
“Amariya, babban firist, shi ne zai shugabance ku a kan dukan al’amuran da suke na wajen Ubangiji, Zebadiya ɗan Ishmayel kuwa, shugabanku a kan dukan al’amuran da suka shafi sarki, Lawiyawa kuma za su zama a matsayin manya a gabanku. Ku yi abubuwa da ƙarfin hali, bari kuma Ubangiji yă kasance tare da masu yin gaskiya.”
A firgice, Yehoshafat ya yanke shawara yă nemi nufin Ubangiji, ya kuma yi shelar azumi a dukan Yahuda.
Mutanen Yahuda suka taru gaba ɗaya don su nemi taimako daga wurin Ubangiji, tabbatacce suka fito daga kowane garin Yahuda don su neme shi.
Sa’an nan Yehoshafat ya miƙe tsaye a taron Yahuda da Urushalima a haikalin Ubangiji a sabon filin
ya ce, “Ya Ubangiji Allah na kakanninmu, ba kai ne Allah wanda yake sama ba? Kana mulki a bisa dukan mulkokin ƙasashe. Iko da girma suna a hannunka, kuma ba wanda zai iya tsayayya da kai.
Ya Allahnmu, ba kai ba ne ka kore mazaunan wannan ƙasa a gaban mutanenka Isra’ila ka kuma ba da ita har abada ga zuriyar Ibrahim abokinka?
Sun yi zama a cikinta suka kuma yi gina wuri mai tsarki a cikinta domin Sunanka cewa,
‘In masifa ta zo mana, ko takobin hukunci, ko annoba ko yunwa, za mu tsaya a gabanka a gaban wannan haikalin da yake ɗauke da Sunanka, mu kuma yi kuka gare ka cikin azaba, za ka kuwa ji mu, ka cece mu.’
“Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra’ilawa su kai musu yaƙi sa’ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra’ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba.
Yau ga yadda suke so su biya mu. Su suke so su kore mu daga ƙasar da ka ba mu gādo.
Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Gama ba mu da ƙarfin fuskantar wannan babbar rundunar da take so ta yaƙe mu. Ba mu san abin da za mu yi ba, mu dai mun zuba maka ido.”
Dukan mazan Yahuda, tare da matansu da yaransu da ƙananansu, suka tsaya a gaban Ubangiji.
Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benahiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, wani Balawe kuma zuriyar Asaf, yayinda yake tsaye a cikin taron.
Ya ce, “Saurara, Sarki Yehoshafat da dukan waɗanda suke zama a Yahuda da Urushalima! Ga abin da Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku ji tsoro ko ku fid da zuciya saboda wannan babbar runduna. Gama yaƙin ba naku ba ne, amma na Allah.
Ba lalle ba ne ku yi wannan yaƙi. Ku dai, ku ja dāgā, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ba ku, ya Yahuda da Urushalima. Kada ku ji tsoro; kada ku karai. Ku fito don ku fuskance su gobe, Ubangiji kuwa zai kasance tare ku.’ ”
Yehoshafat ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, dukan mutanen Yahuda da Urushalima suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada a gaban Ubangiji.
Sa’an nan waɗansu Lawiyawa daga Kohatawa da Korayawa suka tashi tsaye suka yabe Ubangiji, Allah na Isra’ila, da babbar murya sosai.
Da sassafe suka tashi suka nufi Hamadan Tekowa. Yayinda suka kama hanya, Yehoshafat ya tsaya ya ce, “Ku saurare ni, Yahuda da mutanen Urushalima! Ku amince da Ubangiji Allahnku za a kuwa kafa ku; ku amince da annabawansa za ku kuwa yi nasara.”
Bayan suka yi shawara tare da shugabanni, sai ya zaɓi mutanen da za su ja gaban sojoji suna waƙa ga Ubangiji suna yabonsa saboda tsarkinsa suna cewa, “Ku yi godiya ga Ubangiji, gama ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”
Da suka fara waƙa, suna kuma yabo, sai Ubangiji ya kai hari a kan mutanen Ammon da Mowab da Dutsen Seyir, waɗanda suka kawo hari a Yahuda, aka kuwa ci su da yaƙi.