Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Sarki Hezekiya da fadawansa suka umarci Lawiyawa su yabi Ubangiji da kalmomin Dawuda da na Asaf mai duba. Saboda haka suka rera yabai da murna, suka sunkuyar da kawunansu suka yi sujada.

  2. Sa’an nan Hezekiya ya ce, “Yanzu kun keɓe kanku ga Ubangiji. Ku zo ku kuma kawo hadayu da hadayun godiya zuwa ga haikalin Ubangiji.” Saboda haka taron suka kawo hadayu da hadayun godiya, da kuma dukan waɗanda suke da niyya suka kawo hadayun ƙonawa.

  3. Yawan hadayun ƙonawan da taron suka kawo, bijimai saba’in ne, raguna ɗari da kuma bunsurai ɗari biyu, dukansu kuwa domin hadayun ƙonawa ga Ubangiji ne.

  4. Aka kasance da hadayun ƙonawa a yalwace, tare da kitsen hadayun salama da hadayun sha da suke tafe da hadayun ƙonawa. Saboda haka aka sāke kafa hidimar haikalin Ubangiji.

  5. Hezekiya da dukan mutane suka yi farin ciki game da abin da Allah ya yi wa mutanensa, domin ya faru farat ɗaya.

  6. Sai Hezekiya ya aika wa dukan Isra’ila da Yahuda, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa Efraim da Manasse, yana gayyatarsu su zo haikalin Ubangiji a Urushalima, su kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  7. Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba.

  8. Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.

  9. Kada ku zama kamar iyayenku da ’yan’uwanku, waɗanda suka yi rashin aminci ga Ubangiji Allah na kakanninsu, har ya mai da su abin tsoro, yadda kuke gani.

  10. Kada ku yi taurinkai, yadda iyayenku suka yi; ku miƙa kai ga Ubangiji. Ku zo wuri mai tsarki, wanda ya tsarkake har abada. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin fushi mai zafi yă juye daga gare ku.

  11. In kuka dawo wurin Ubangiji, sa’an nan waɗanda suka kama ’yan’uwanku da ’ya’yanku za su nuna musu tausayi, su kuma dawo wannan ƙasa, gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne mai jinƙai kuma. Ba zai kau da fuskarsa daga gare ku ba, in kuka dawo gare shi.”

  12. Haka ma a Yahuda, hannun Allah yana a kan mutane don yă ba su zuciya ɗaya su yi abin da sarki da fadawansa suka umarta, suna bin maganar Ubangiji.

  13. Suka yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu na wata na biyu. Firistoci da Lawiyawa suka ji kunya suka tsarkake kansu, suka kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji.

  14. Sa’an nan suka ɗauki matsayinsu na kullum yadda yake a Dokar Musa mutumin Allah. Firistoci suka yayyafa jinin da Lawiyawa suka ba su.

  15. Da yake da yawa cikin taron ba su tsarkake kansu ba, dole Lawiyawa su yanka ’yan ragunan Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda ba su da tsarki, ba su kuma iya tsarkake ragunansu ga Ubangiji ba.

  16. Ko da yake yawancin mutanen da suka zo daga Efraim, Manasse, Issakar da Zebulun ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci Bikin Ƙetarewa, ba tare da bin abin da yake a rubuce ba. Amma Hezekiya ya yi addu’a dominsu cewa, “Bari Ubangiji, wanda yake nagari, yă gafarta wa kowa

  17. wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko da shi marar tsarki ne bisa ga dokokin wuri mai tsarki.”

  18. Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya ya kuma warkar da mutane.

  19. Isra’ilawan da suka kasance a Urushalima suka yi Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai da farin ciki mai girma, yayinda Lawiyawa da firistoci suke rera ga Ubangiji kowace rana, haɗe da kayan kiɗin yabon Ubangiji.

  20. Hezekiya ya yi magana mai ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna ganewar fasaha a hidimar Ubangiji. Kwana bakwai suka ci rabonsu da aka tsara, suka miƙa hadayun salama, suka kuma yabi Ubangiji Allah na kakanninsu.

  21. Firistoci da Lawiyawa suka tsaya suka albarkace mutane, Allah kuma ya ji su, gama addu’arsu ya kai sama, mazauninsa mai tsarki.

  22. Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi-kashi, kowanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima, su yi godiya, su kuma rera yabai a ƙofofin mazaunin Ubangiji.

  23. Sarki ya ba da taimako daga mallakarsa domin hadayun ƙonawa, safe da yamma da kuma don hadayun ƙonawa a Asabbatai, Sabon Wata da kuma ƙayyadaddun bukukkuwa kamar yadda yake a rubuce a cikin Dokar Ubangiji.

  24. Ya umarci mutanen da suke zama a Urushalima su ba da rabon da yake na firistoci da Lawiyawa, don su ƙwallafa ransu ga Dokar Ubangiji.

  25. Mutanen Isra’ila da Yahuda waɗanda suke zama a garuruwan Yahuda, su ma suka kawo zakan shanu da na tumaki da kuma zakan abubuwa masu tsarki da aka keɓe ga Ubangiji Allahnsu, suka jibge su tsibi-tsibi.