Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Time

82 ayoyi · 44 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A shekara ta talatin, a wata na huɗu a rana biyar, yayinda nake cikin ’yan zaman bauta kusa da Kogin Kebar, sai sammai suka buɗe na kuwa ga wahayoyin Allah.

  2. A shekara ta goma sha biyu ta zaman bautanmu, a wata na goma a rana ta biyar, wani mutumin da ya gudu daga Urushalima ya zo wurina ya ce, “Birnin ya fāɗi!”

  3. A shekara ta ashirin da biyar ta zaman bauta, a farkon shekara, a rana ta goma ga wata, a shekara ta goma sha huɗu bayan fāɗuwar birnin Urushalima, a wannan rana ikon Ubangiji ya sauko a kaina ya kuma iza ni.

  4. Nan da nan sai ga yatsotsin hannun mutum sun bayyana, suna yin rubutu a kan shafen bangon, kusa da wurin da ake ajiye fitilar fadar sarki. Sarki kuwa yana ganin hannun yayinda yake rubutu.

  5. Zai yi maganar saɓo a kan Mafi Ɗaukaka, zai kuma tsananta wa tsarkaka yă kuma yi ƙoƙarin sāke lokuta da shari’u. Za a miƙa tsarkaka a hannunsa na wani lokaci, lokuta da kuma rabin lokaci.

  6. a shekara ta farko ta mulkinsa, ni, Daniyel na gane daga cikin littattafai, bisa ga maganar Ubangiji da aka faɗa wa annabi Irmiya, cewa zaman Urushalima kango zai kai shekara saba’in.

  7. A wannan lokaci ni Daniyel na yi makoki har na sati uku.

  8. Mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, ya ɗaga hannun damansa da kuma na hagunsa sama, sai na ji yana rantsuwa da wannan da yake raye har abada, yana cewa, “Zai kasance na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa’ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”

  9. Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.

  10. Yana cewa, “Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”

  11. Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su,

  12. A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline.

  13. Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya.

  14. Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya.

  15. Ka ba mu kowace rana abincin yini.

  16. Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’

  17. Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan.

  18. Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji,

  19. Dole yă kasance a sama, sai lokaci ya yi da Allah zai mai da kome sabo, yadda ya yi alkawari tun dā ta wurin annabawansa masu tsarki.

  20. Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance.

  21. farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu.

  22. Gama ya ce, “A lokacin samun alherina, na ji ka, a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.” Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto.

  23. Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka,

  24. Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.

  25. Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.