Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Time: Part of a period of, usually counted as the whole
Ayoyi game da Part of a period of, usually counted as the whole
Shawulu yana da shekara talatin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarautar Isra’ila shekara arba’in da biyu.
“Ka tafi, ka tattara dukan Yahudawan da suke Shusha, ku yi azumi saboda ni. Kada ku ci ko ku sha, dare da rana har kwana uku. Ni kuwa da bayina za mu yi azumi yadda kuke yi. Idan aka yi haka, zan tafi wurin sarki, ko da yake wannan karya doka ce. Idan na hallaka, to, na hallaka.”
A rana ta uku, Esta ta sanya rigunanta na sarauta, ta tafi ta tsaya a harabar fada, a gaban zaure sarki. Sarki yana zaune a kan gadon sarautarsa a zauren, yana fuskantar ƙofar shiga.