Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Time

82 ayoyi · 44 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi.

  2. Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.

  3. Waɗannan ƙa’idodi sun shafi sha’anin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙa’idodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau.

  4. Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma.

  5. Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne.

  6. Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri!

  7. Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba.