Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribe Of Reuben

119 ayoyi · 24 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma in ba su haye tare da ku da shirin yaƙi ba, to, sai ku ba su gādo a wancan haye kamar sauran kabilun a Kan’ana.”

  2. Mutanen Gad da mutanen Ruben suka amsa, suka ce, “Barorinka za su yi abin da Ubangiji ya faɗa.

  3. Za mu haye a gaban Ubangiji zuwa Kan’ana, amma mallakarmu ta gādo, za tă kasance a wannan hayi na Urdun.”

  4. Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye.

  5. Mutanen Ruben suka sāke gina Heshbon, Eleyale, da Kiriyatayim,

  6. haka kuma suka gina Nebo da Ba’al-Meyon (an canja waɗannan sunaye) suka kuma gina Sibma. Suka ba wa biranen da suka sāke ginawa sunaye.

  7. Amma ga mutanen Ruben da mutanen Gad, na ba da yankin da ya tashi daga Gileyad, ya gangara zuwa Kwarin Arnon (tsakiyar kwarin kuwa shi ne iyaka) ya fita zuwa Kogin Yabbok, wanda yake shi ne iyakar Ammonawa.

  8. Iyakarsa daga yamma kuwa shi ne Urdun a Araba, daga Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri) a gangaren gindin Dutsen Fisga wajen gabas.

  9. Na umarce ku a lokacin na ce, “Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban ’yan’uwanku, Isra’ilawa.

  10. Amma matanku, yaranku da dabbobinku (na sani kuna da dabbobi masu yawa), su ne za ku bari a garuruwan da na ba ku,

  11. sai Ubangiji ya ba da hutu ga sauran ’yan’uwanku, yadda ya yi da ku, su ma suka sami ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba su, a ƙetaren Urdun, sa’an nan kowannenku zai komo ga mallakar da na ba ku.”

  12. Waɗannan kabilai kuma za su tsaya a bisa Dutsen Ebal su furta la’ana, wato, kabilar Ruben, Gad, Asher, Zebulun, Dan da Naftali.

  13. “Bari Ruben yă rayu, kada yă mutu, kada mutanensa su zama kaɗan.”

  14. Ga abin da Musa ya ba kabilar Ruben bisa ga iyalansu.

  15. Abin da ya kama daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba

  16. zuwa Heshbon, da dukan garuruwan kan tudu, haɗe da Dibon, Bamot Ba’al, Bet-Ba’al-Meyon,

  17. Yahza, Kedemot, Mefa’at,

  18. Kiriyatayim, Sibma, Zeret Shahar kan tudu cikin kwari,

  19. Bet-Feyor, gangaren Fisga da Bet-Yeshimot,

  20. dukan garuruwan da suke kan tudu da dukan masarautar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Musa ya yi nasara da shi, da shugabannin Midiyawa, wato, Ewi, Rekem, Zur, Hur, da Reba, sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.

  21. Ƙari a kan waɗanda aka kashe a yaƙi, Isra’ilawa suka kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi don yana duba.

  22. Gefen Urdun shi ne iyakar mutanen Ruben. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon mutanen Ruben, bisa ga iyalansu.

  23. Yoshuwa ya kira mutanen Ruben, mutanen Gad, da rabin kabilar Manasse

  24. ya ce musu, “Kun yi duk abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta, kun kuma yi mini biyayya cikin dukan umarnan da na ba ku.

  25. Dukan waɗannan yawan kwanaki, har zuwa yau, ba ku yashe ’yan’uwanku Isra’ilawa ba, amma kuka kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnku ya ba ku.