Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Slander

116 ayoyi · 71 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu.

  2. Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa, Ya kai harshe mai ruɗu!

  3. Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba.

  4. gama mugaye da masu ruɗu sun buɗe bakunansu a kaina; sun yi magana a kaina da harsunan ƙarya.

  5. Da kalmomin ƙiyayya sun kewaye ni; sun tasar mini ba dalili.

  6. Bari wannan yă zama sakayyar Ubangiji ga masu zargina, ga waɗanda suke mugayen maganganu a kaina.

  7. Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji; dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. Sela

  8. Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

  9. mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

  10. Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa, duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne.

  11. Da bakinsa marar sanin Allah kan hallaka maƙwabcinsa, amma ta wurin sani mai adalci kan kuɓuta.

  12. Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi, amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.

  13. Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.

  14. Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.

  15. Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke; sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum.

  16. Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini haka yake da mutumin da yake ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinsa.

  17. Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi.

  18. In ba itace wuta takan mutu; haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.

  19. Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi; sukan gangara can cikin cikin mutum.

  20. In maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi, ina amfanin maganin?

  21. Farkon maganarsa wauta ce, ƙarshenta kuma takan zama muguwar hauka,

  22. Su duka masu taurinkai ne, ’yan tawaye, suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da ƙarfe; dukansu lalatattu ne.

  23. “Ka yi hankali da abokanka; kada ka amince da ’yan’uwanka. Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne, kowane aboki kuma mai kushe ne.

  24. Na ji mutane da yawa suna raɗa cewa, “Razana ta kowace fuska! Mu kai kararsa! Bari mu kai kararsa!” Dukan abokaina suna jira in yi tuntuɓe, suna cewa, “Mai yiwuwa a ruɗe shi; sai mu yi nasara a kansa mu ɗau fansa a kansa.”

  25. Sai fadawa suka ce wa sarki, “Ya kamata a kashe wannan mutum. Yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran mutane, ta wurin abubuwan da yake faɗa musu. Wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan sai dai wahala.”