Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Slander: Unclassified scriptures relating to

27 ayoyi · 71 fannoni

Ayoyi game da Unclassified scriptures relating to

Tace bisa littafi
  1. “Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya.

  2. In mutum ya auri mace, bayan ya kwana da ita, sa’an nan ya ƙi ta

  3. ya kuma zarge ta, ya ba ta mummunan suna, yana cewa, “Na auri wannan mata, amma sa’ad da na kusace ta, ban sami tabbaci cewa ita budurwa ba ce,”

  4. sai mahaifin yarinyar da mahaifiyarta su kawo shaida cewa ita budurwa ce wa dattawan gari a ƙofar garin.

  5. Mahaifin yarinyar zai ce wa dattawa, “Na ba da ’yata aure ga wannan mutum, amma ya ƙi ta.

  6. Yanzu ya zage ta cewa, ‘Ban sami ’yarku budurwa ba.’ Amma ga shaidar budurcin ’yata.” Sa’an nan iyayenta za su shimfiɗa zanen a gaban dattawan garin,

  7. dattawan kuwa za su ɗauki mutumin su hukunta shi.

  8. Za su ci masa tara shekel azurfa ɗari, su ba mahaifin yarinyar, domin wannan mutum ya ba wa budurwa mutuniyar Isra’ila mummunan suna. Za tă ci gaba da zama matarsa; ba kuwa zai sake ta ba muddin ransa.

  9. Zai kāre ka daga ɓata suna, kuma ba ka bukata ka ji tsoro in hallaka ta zo.

  10. Duk sa’ad da wani ya zo ganina, yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi; sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.

  11. Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina; suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa,

  12. “Mugun ciwo ya kama shi; ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.”

  13. Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni.

  14. Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku.

  15. Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba.

  16. Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa, duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne.

  17. Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi.

  18. Su duka masu taurinkai ne, ’yan tawaye, suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da ƙarfe; dukansu lalatattu ne.

  19. “Ka yi hankali da abokanka; kada ka amince da ’yan’uwanka. Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne, kowane aboki kuma mai kushe ne.

  20. Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne,

  21. da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu;

  22. in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yă zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.

  23. ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.

  24. Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi.

  25. ’Yan’uwa, kada ku ɓata wa juna suna. Duk wanda ya zargi ɗan’uwansa ko ya ɗora masa laifi, yana gāba da doka ne yana kuma yin mata shari’a ke nan. In kuwa ka ɗora wa shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.