Skip to content

Rehum

4 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Rehum

  1. Rehum shugaban rundunar soja, da Shimshai marubuci, suka rubuta wasiƙar a kan Urushalima zuwa ga sarki Artazerzes, suka ce.

  2. Rehum shugaban sojoji, da Shimshai marubuci, da sauran abokansu, wato, alƙalai, da masu riƙe da muƙamai daga Farisa, Uruk da Babilon, mutanen Elam da na Shusha,

  3. Sarki ya aika da wannan amsa. Zuwa ga Rehum shugaban sojoji, Shimshai marubuci da kuma sauran abokansu waɗanda suke zama a Samariya da kuma sauran wurare a Kewayen Kogin Yuferites. Gaisuwa.

  4. Da gama karanta wasiƙar sarki Artazerzes wa Rehum da Shimshai marubuci, da abokansu, sai suka yi sauri suka je wurin Yahudawa a Urushalima, suka hana su aikin ƙarfi da yaji.