Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Slander

116 ayoyi · 71 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yaƙub ya ji cewa ’ya’ya Laban mazan suna cewa, “Yaƙub ya kwashe dukan abin da mahaifinmu yake da shi, ya kuma sami dukan wannan arziki daga abin da yake na mahaifinmu.”

  2. Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.

  3. “Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya.

  4. “ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.

  5. Kada ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka.

  6. In wani ɗan sharri ya tashi ya yi wa wani sharri, don a sami wani da laifi,

  7. dole mutanen nan biyu da suke rikici su tsaya a gaban Ubangiji, a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin.

  8. Dole alƙalan su yi bincike sosai, in kuma aka tabbatar mai ba da shaida maƙaryaci ne, yana ba da shaidar zur a kan ɗan’uwansa ne,

  9. to, sai a yi da shi yadda ya yi niyya yă yi da ɗan’uwansa. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

  10. Sauran mutane za su ji wannan su kuma ji tsoro, ba kuwa za a ƙara yin irin wannan mugun abu a cikinku ba.

  11. Kada ku ji tausayi, rai yă zama a maimakon rai, ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa.

  12. In mutum ya auri mace, bayan ya kwana da ita, sa’an nan ya ƙi ta

  13. ya kuma zarge ta, ya ba ta mummunan suna, yana cewa, “Na auri wannan mata, amma sa’ad da na kusace ta, ban sami tabbaci cewa ita budurwa ba ce,”

  14. sai mahaifin yarinyar da mahaifiyarta su kawo shaida cewa ita budurwa ce wa dattawan gari a ƙofar garin.

  15. Mahaifin yarinyar zai ce wa dattawa, “Na ba da ’yata aure ga wannan mutum, amma ya ƙi ta.

  16. Yanzu ya zage ta cewa, ‘Ban sami ’yarku budurwa ba.’ Amma ga shaidar budurcin ’yata.” Sa’an nan iyayenta za su shimfiɗa zanen a gaban dattawan garin,

  17. dattawan kuwa za su ɗauki mutumin su hukunta shi.

  18. Za su ci masa tara shekel azurfa ɗari, su ba mahaifin yarinyar, domin wannan mutum ya ba wa budurwa mutuniyar Isra’ila mummunan suna. Za tă ci gaba da zama matarsa; ba kuwa zai sake ta ba muddin ransa.

  19. Amma Doyeg mutumin Edom da yake tsaye tare da fadawan Shawulu ya ce, “Na ga ɗan Yesse ya zo wurin Ahimelek ɗan Ahitub a Nob.

  20. Ahimelek ya roƙi Ubangiji saboda shi, ya kuma ba shi guzuri da takobin Goliyat Bafilistin.”

  21. Sai sarki ya aika aka kira masa Ahimelek firist ɗan Ahitub da dukan iyalin mahaifinsa. Dukansu suka zo wurin sarki.

  22. Ya ce wa Shawulu, “Me ya sa kake saurari mutanen da suke cewa, ‘Dawuda ya dāge yă cuce ka’?

  23. sai manyan mutanen Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aiko da jakadu su kawo maka ta’aziyya? Ai, wayo ya yi don yă ga asirin birninmu, yă san ƙarfinmu, yă kuma ci mu da yaƙi.”

  24. Sai sarki ya ce, “Ina jikar maigidanka?” Ziba ya ce, “Yana zaune a Urushalima gama yana tsammani cewa, ‘Yau gidan Isra’ila za su mayar mini da sarautar kakana.’ ”

  25. Sa’an nan ’yan iska biyu suka zo, suka zauna ɗaura da shi, suka kawo zarge a kan Nabot a gaban mutane, suna cewa, “Nabot ya zagi Allah da sarki.” Saboda haka aka ɗauke shi waje da birnin, aka jajjefe shi da dutse har ya mutu.