Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Slander

116 ayoyi · 71 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A cikinki akwai mutane waɗanda suka nace su yi kisankai; a cikinki akwai waɗanda suke ci a dutsen tsafi suna yin ayyukan lalata.

  2. “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.

  3. Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’

  4. Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”

  5. Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa.

  6. Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.

  7. Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.

  8. Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito. A ƙarshe, biyu suka zo gaba,

  9. suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”

  10. Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa.

  11. Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”

  12. Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.”

  13. Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.”

  14. Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.”

  15. Sa’ad da aka shigo da Bulus, sai Tertullus ya shiga kai ƙararsa a gaban Felis yana cewa, “Mun daɗe muna zaman lafiya a ƙarƙashinka, hangen nesanka kuma ya kawo gyare-gyare a wannan ƙasa.

  16. “Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana tā-da-na-zaune-tsaye a tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa

  17. Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne,

  18. da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu;

  19. In haka ne, “Ba sai mu yi ta yin mugunta don yă zama hanyar samun nagarta ba”? Kamar yadda masu baƙar magana game da mu suna cewa wai haka muke faɗa. Tabbatacce za a hukunta irin waɗannan da hukuncin da ya dace da su.

  20. in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yă zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.

  21. ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.

  22. ta wurin ɗaukaka da ƙasƙanci, da cikin ɓata suna, da kuma cikin yabo. Cikin faɗin gaskiya, an ɗauke mu masu ƙarya,

  23. Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi.

  24. Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta.

  25. A haka kuma, dole matansu su zama matan da suka cancanci girmamawa, ba masu gulma ba, sai dai masu sauƙinkai da kuma masu aminci a cikin kome.