Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings

802 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa, bebaye kuma su yi sowa don farin ciki. Ruwa zai kwararo daga jeji rafuffuka kuma a cikin hamada.

  2. Yashi mai ƙuna zai zama tafki, ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za tă cika da maɓulɓulan rafuffuka. A mazaunin diloli, inda suka taɓa zama, ciyawa da iwa da kyauro za su yi girma.

  3. Kuma babbar hanya za tă kasance a can; za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki. Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba; za tă zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce; mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba.

  4. Zaki ba zai kasance a can ba, balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta; ba za a same su a can ba. Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can,

  5. kuma fansassu na Ubangiji za su komo. Za su shiga Sihiyona da rerawa; matuƙar farin ciki zai mamaye su. Murna da farin ciki za su sha kansu, baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.

  6. Ta’aziyya, ku ta’azantu mutanena, in ji Allahnku.

  7. Yi magana mai kwantar da rai ga Urushalima, ku kuma furta mata cewa aiki mai zafinta ya isa, cewa an fanshi zunubinta, cewa ta karɓi daga hannun Ubangiji ninki biyu saboda dukan zunubanta.

  8. Muryar wani tana kira cewa, “A cikin hamada ku shirya hanya saboda Ubangiji; ku miƙe manyan hanyoyi domin Allahnmu a cikin jeji.

  9. Za a cike kowane kwari, a baje kowane dutse da kowane tudu; za a mayar da karkatattun wurare su zama sumul, munanan wurare kuma su zama da kyau.

  10. Za a kuma bayyana ɗaukakar Ubangiji, dukan mutane kuwa za su gan ta. Gama Ubangiji da kansa ne ya yi magana.”

  11. Muryar tana cewa, “Ka yi shela.” Na kuwa ce, “Me zan yi shelar?” “Dukan mutane kamar ciyawa suke, kuma dukan ɗaukakarsu kamar furannin jeji ne.

  12. Ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi, domin Ubangiji ya hura iska a kansu. Tabbatacce mutane ciyawa ne.

  13. Hakika ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi, amma maganar Allahnmu tana nan daram har abada.”

  14. Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Sihiyona, ka haura a bisa dutse. Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Urushalima, ka tā da muryarka ka yi ihu, ka ɗaga ta, kada ka ji tsoro; faɗa wa garuruwan Yahuda, “Ga Allahnku!”

  15. Duba, Ubangiji Mai Iko Duka yana zuwa da iko, hannunsa kuma yana yin mulki dominsa. Duba, ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa kuma na rakiyarsa.

  16. Yakan lura da garkensa kamar makiyayi. Yakan tattara tumaki wuri ɗaya yă riƙe su kurkusa da ƙirjinsa; a hankali kuma yakan bi da masu ba da mama.

  17. Wane ne ya auna ruwaye a tafin hannunsa, ko kuwa ya gwada tsawon sammai da fāɗin tafin hannunsa? Wane ne ya riƙe ƙurar ƙasa a kwando, ko kuwa ya auna nauyin duwatsu a magwaji, tuddai kuma a ma’auni?

  18. Wane ne ya fahimci zuciyarUbangiji, ko kuwa ya koya masa a matsayin mashawarcinsa?

  19. Wane ne Ubangiji ya nemi shawararsa don yă ganar da shi, wane ne kuma ya koya masa hanyar da ta dace? Wane ne ya koya masa sani ko ya nuna masa hanyar fahimta?

  20. Tabbatacce al’ummai suna kama da ɗigon ruwa a cikin bokiti an ɗauke su a matsayin ƙura a kan magwaji; yakan auna tsibirai sai ka ce ƙura mai laushi.

  21. Itatuwan Lebanon ba su isa a yi wutar bagade da su ba, balle dabbobinsa su isa yin hadayun ƙonawa.

  22. A gabansa dukan al’ummai ba kome ba ne; ya ɗauke su ba a bakin kome ba kuma banza ne kurum.

  23. To, ga wane ne za ka kwatanta Allah? Wace siffa za ka kwatanta shi da ita?

  24. Gunki dai, maƙeri kan yi zubinsa, maƙerin zinariya kuma yă ƙera shi da zinariya yă kuma sarrafa masa sarƙoƙin azurfa.

  25. Mutumin da talauci ya sha kansa da ba zai iya miƙa irin hadayar nan ba kan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yakan nemi gwanin sassaƙa don yă sassaƙa masa gunkin da ba zai fāɗi ba.