Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings

802 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Hanyoyinka, ya Allah, masu tsarki ne. Wanda allah ne yake da girma kamar Allahnmu?

  2. Kai ne Allahn da yakan aikata mu’ujizai; ka nuna ikonka a cikin mutane.

  3. Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka, zuriyar Yaƙub da Yusuf. Sela

  4. Ruwaye sun gan ka, ya Allah, ruwaye sun gan ka suka firgita; zurfafan gaske sun girgiza.

  5. Gizagizai sun sauko da ruwa, sararin sama suka buga tsawa; kibiyoyinka suka yi ta kai komo da walƙiya.

  6. Aka ji tsawanka a cikin guguwa, walƙiyarka ta haskaka duniya; duniya ta yi rawar jiki ta girgiza.

  7. Hanyarka ta bi ta cikin teku, hanyarka ta bi cikin manyan ruwaye, duk da haka ba a ga sawunka ba.

  8. Ka bi da mutanenka kamar garke ta hannun Musa da Haruna.

  9. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Na ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ina misalin kyan wurin zamanka, Ya Ubangiji Maɗaukaki!

  10. Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai.

  11. Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna.

  12. Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. Sela

  13. Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka, waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne.

  14. Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka, sukan mai da shi wurin maɓulɓulai; ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna.

  15. Suna ta ƙara ƙarfi, har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona.

  16. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. Sela

  17. Ka dubi garkuwarmu, ya Allah; ka duba da alheri a kan shafaffenka.

  18. Rana guda a filayen gidan sun fi dubu a wani wuri dabam; zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna da in zauna a tentunan mugaye.

  19. Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa; Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja; ba ya hana kowane abu mai kyau wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

  20. Ya Ubangiji Maɗaukaki, mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.

  21. Zabura ce. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto.

  22. Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.

  23. Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu.

  24. Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;

  25. ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa,