Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings

802 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai girma a yaƙi.

  2. Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.

  3. Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji Maɗaukaki, shi ne Sarkin ɗaukaka. Sela

  4. Zabura ta Dawuda. Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya, ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.

  5. Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.

  6. Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye; Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.

  7. Muryar Ubangiji mai iko ce; muryar Ubangiji da girma take.

  8. Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.

  9. Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi, Siriyon kuma kamar ɗan jakin jeji.

  10. Muryar Ubangiji ta buga da walƙatar walƙiya.

  11. Muryar Ubangiji ta girgiza hamada Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.

  12. Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak ya kakkaɓe itatuwan kurmi. Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”

  13. Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa; Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.

  14. Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa; Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.

  15. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

  16. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,

  17. ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela

  18. Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.

  19. Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe.

  20. Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi; ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.

  21. Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

  22. Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya.

  23. Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta.

  24. “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.”

  25. Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela