Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings

802 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.

  2. Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa,

  3. “Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.”

  4. Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji. Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne; yau na zama Mahaifinka.

  5. Ka tambaye ni zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka, iyakokin duniya su zama mallakarka.

  6. Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe; za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.”

  7. Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo; ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya.

  8. Ku bauta wa Ubangiji da tsoro ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.

  9. Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushi ku hallaka a abubuwan da kuke yi, gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya. Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.

  10. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai.

  11. Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru.

  12. Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,

  13. wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi?

  14. Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.

  15. Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,

  16. dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji,

  17. tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.

  18. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya!

  19. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Ya rera ta ga Ubangiji kalmomin wannan waƙa sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa da kuma daga hannun Shawulu, ya ce, Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina.

  20. Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka. Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata.

  21. Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa kuɓuta daga abokan gābana.

  22. Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni; rigyawan hallaka sun sha kaina.

  23. Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni; tarkon mutuwa ya yi mini arangama.

  24. Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; Na yi kuka ga Allahna don taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.

  25. Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, tussan duwatsu sun girgiza; sun yi rawa domin ya yi fushi.