Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings

802 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mutum bai gane muhimmancinta ba, ba a samunta a ƙasar masu rai.

  2. Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”; teku ya ce, “Ba ta wurina.”

  3. Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta, ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.

  4. Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir, ko sauran duwatsu masu daraja ba.

  5. Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba, ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.

  6. Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya; farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai.

  7. Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba, zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba.

  8. “To, daga ina ke nan hikima ta fito? Ina fahimta take zama?

  9. An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai, har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita.

  10. Hallaka da mutuwa suna cewa, ‘Jita-jitarta kaɗai muke ji.’

  11. Allah ya gane hanyar zuwa wurinta. Shi ne kaɗai ya san inda take zama,

  12. Gama yana ganin iyakar duniya kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama.

  13. Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura, ya kuma auna ruwaye.

  14. Lokacin da ya yi wa ruwan sama doka da kuma hanya domin walƙiya,

  15. sai ya dubi hikima ya auna ta; ya tabbatar da ita, ya gwada ta.

  16. Ya kuma ce wa mutum, ‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima, kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”

  17. Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a.

  18. Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana.

  19. Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

  20. Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa.

  21. Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai.

  22. Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

  23. Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?

  24. Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.

  25. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.”