Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings

802 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Hayaƙi ya tashi daga kafan hancinsa; wuta mai ci daga bakinsa, garwashi wuta mai ci daga bakinsa.

  2. Ya buɗe sammai ya sauko; baƙaƙen gizagizai suna a ƙarƙashin ƙafafunsa.

  3. Ya hau kerubobi ya kuma yi firiya; ya yi shawagi a fikafikan iska.

  4. Ya mai da duhu abin rufuwarsa, rumfa kewaye da shi, baƙaƙen gizagizan ruwan sama na sarari,

  5. daga cikin hasken kasancewarsa gizagizai suka yi gaba, da ƙanƙara da kuma walƙiya.

  6. Ubangiji ya yi tsawa daga sama; muryar Mafi Ɗaukaka ya yi kāra.

  7. Ya harba kibiyoyinsa ya kuma watsar da abokan gāba, walƙiya mai girma ya fafare su.

  8. Kwarin teku sun bayyana tussan duniya sun bayyana a fili sa’ad da ka tsawata, ya Ubangiji, sa’ad da ka numfasa daga hancinka.

  9. Ya miƙa hannunsa daga sama ya kama ni; ya ja ni daga zurfin ruwaye.

  10. Ya cece ni daga abokin gābana mai ƙarfi, daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina.

  11. Sun yi arangama da ni a ranar masifa, amma Ubangiji ya zama mai taimakona.

  12. Ya fitar da ni zuwa wuri mai sarari; ya kuɓutar da ni, gama yana jin daɗina.

  13. Zabura ta Dawuda. Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

  14. Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa, yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

  15. yakan maido da raina. Yakan bi da ni a hanyoyin adalci saboda sunansa.

  16. Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya.

  17. Ka shirya mini tebur a gaban abokan gābana. Ka shafe kaina da mai; kwaf nawa ya cika har yana zuba.

  18. Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi dukan kwanakin raina, zan kuwa zauna a gidan Ubangiji har abada.

  19. Zabura ta Dawuda. Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;

  20. gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye.

  21. Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?

  22. Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.

  23. Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.

  24. Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan, waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. Sela

  25. Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.