Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings

802 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Rana da wata suka tsaya cik a sammai da ganin kibiyoyinka masu wucewa fyu, da ganin hasken māshinka mai walƙiya.

  2. Cikin hasala ka ratsa duniya cikin fushi kuma ka tattake ƙasashe.

  3. Ka fito don ka fanshi mutanenka, don ceci shafaffenka. Ka ragargaza shugaban ƙasar mugaye, ka tuɓe shi daga kai har ƙafa. Sela

  4. Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa,

  5. sai ya fara koya musu. Yana cewa,

  6. “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu, gama mulkin sama nasu ne.

  7. Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu ta’aziyya.

  8. Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u, gama za su gāji duniya.

  9. Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci, gama za a ƙosar da su.

  10. Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai.

  11. Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.

  12. Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su ’ya’yan Allah.

  13. Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci, gama mulkin sama nasu ne.

  14. “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.

  15. Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

  16. “Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.

  17. “Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa.

  18. Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida.

  19. Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.

  20. Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba?

  21. Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?

  22. “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa.

  23. Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba.

  24. In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?

  25. Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’