Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings

802 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu.

  2. Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.

  3. Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.

  4. “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama.

  5. Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’

  6. Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’

  7. “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.

  8. Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse.

  9. Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi.

  10. Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”

  11. Sai Maryamu ta ce, “Raina yana ɗaukaka Ubangiji

  12. ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,

  13. gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa. Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,

  14. gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa, sunansa labudda Mai Tsarki ne.

  15. Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa, daga zamani zuwa zamani.

  16. Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa; ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu.

  17. Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.

  18. Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa amma ya sallami mawadata hannu wofi.

  19. Ya taimaki bawansa Isra’ila, yana tunawa yă nuna jinƙai

  20. ga Ibrahim da zuriyarsa har abada, kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.”

  21. Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku sa’an nan ta koma gida.

  22. Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce,

  23. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.

  24. Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda

  25. (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),