Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Judgments

271 ayoyi · 91 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Aka ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji. Aka kuma kashe ’ya’yan Eli biyu, Hofni da Finehas.

  2. A wannan rana wani mutumin Benyamin ya ruga da bakin dāgā ya shigo Shilo, taguwarsa a yage, kansa kuma a rufe da ƙasa.

  3. Da ya iso sai ga Eli zaune a kujera kusa da hanya yana kallo, domin tsoron da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shigo a garin ya ba da labarin abin da ya faru sai dukan gari ya ruɗe da ihu.

  4. Eli ya ji ihun ya yi tambaya ya ce, mene ne dalilin wannan ihu? Mutumin ya rugo wurin Eli,

  5. wanda yake da shekaru tasa’in da takwas da haihuwa, idanunsa kuma ƙarfi ya ƙare, baya iya gani.

  6. Mutumin ya gaya wa Eli cewa, “Shigowata ke nan daga bakin dāgā. Na kuɓuce daga can yau ɗin nan.” Eli ya ce, “Me ya faru da ’ya’yana?”

  7. Mutumin da ya kawo labarin ya ce, “Isra’ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, mayaƙan kuma sun sha mummunar ɗibga. ’Ya’yanka Hofni da Finehas su ma sun mutu. Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

  8. Da ya ambaci akwatin alkawarin Allah, sai Eli ya fāɗi da baya daga kujeransa kusa da ƙofa, wuyarsa ta karye, ya kuma mutu domin ya tsufa ƙwarai. Ya yi shugabancin Isra’ila shekaru arba’in.

  9. Matar Finehas, ɗansa tana da ciki a lokacin ta kuma kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari cewa an ƙwace akwatin alkawarin Allah, ta kuma labarin surukinta da mijinta sun mutu, sai ta shiga naƙuda, ta kuma haihu. Amma naƙuda ta sha ƙarfinta.

  10. Da tana mutuwa, matan da suke lura da ita suka ce, “Kada ki karaya kin haifi ɗa namiji.” Amma ba tă ba da amsa ko tă kula ba.

  11. Ta ba wa yaron suna Ikabod, ma’ana “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila”, domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma mutuwar surukinta da na mijinta.

  12. Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

  13. Bisa ga umarnin Ubangiji, sai wani mutumin Allah ya zo daga Yahuda zuwa Betel, yayinda Yerobowam yake tsaye kusa da bagade don yă miƙa hadaya.

  14. Sai mutumin Allah ya tā da murya a kan bagade bisa ga umarnin Ubangiji ya ce, “Ya bagade, bagade! Ubangiji ya ce, ‘Za a haifi ɗa mai suna Yosiya wa gidan Dawuda. A kanka zai miƙa firistoci na masujadai kan tuddai masu miƙa hadayu a nan, za a kuma ƙone ƙasusuwan mutane a kanka.’ ”

  15. A wannan rana mutumin Allah ya ba da alama, “Ga alamar da Ubangiji ya furta. Wannan bagade zai tsage yă rabu kashi biyu, tokar da yake a kansa za tă zuba a ƙasa.”

  16. Sa’ad da Yerobowam ya ji abin da mutumin Allah ya tā da murya ya faɗa game da bagaden Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden ya ce, “Ku kama shi!” Amma sai hannun da ya miƙa ya yanƙwane, har bai iya janye shi ba.

  17. Haka ma, bagaden ya rabu, tokarsa kuma ya zuba, bisa ga alamar da mutumin Allah ya bayar, ta wurin kalmar Ubangiji.

  18. Sai sarki ya ce wa mutumin Allah, “Ka roƙi Ubangiji Allahnka, ka kuma yi addu’a domina don hannuna ya warke.” Saboda haka mutumin Allah ya yi roƙo ga Ubangiji, hannun sarki kuwa ya warke, ya kuma zama kamar yadda yake a dā.

  19. Sai sarki ya ce wa mutumin Allah, “Zo gida tare da ni, ka sami wani abu ka ci, zan kuwa yi maka kyauta.”

  20. Amma mutumin Allah ya amsa wa sarki, “Ko da za ka ba rabin mallakarka, ba zan tafi tare da kai ba, ba kuwa zan ci abinci, ko in sha ruwa a can ba.

  21. Gama an umarce ni ta wurin kalmar Ubangiji, aka ce, ‘Kada ka ci abinci, ko ka sha ruwa, ko ka koma ta hanyar da ka zo.’ ”

  22. Saboda haka ya ɗauki wata hanya, bai kuwa koma ta hanyar da ya zo Betel ba.

  23. To, fa, akwai wani tsohon annabi yana zama a Betel, wanda ’ya’yansa suka zo suka faɗa masa dukan abin da mutumin Allah ya yi a can, a ranar. Suka kuma faɗa wa mahaifinsu abin da ya faɗa wa sarki.

  24. Mahaifinsu ya tambaye su ya ce, “Wace hanya ce ya bi?” Sai ’ya’yansa suka nuna masa hanyar da mutumin Allah daga Yahuda ya bi.

  25. Sai ya ce wa ’ya’yansa, “Ku yi wa jakina shimfiɗa.” Da suka yi wa jakin shimfiɗa, sai ya hau.