Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Judgments

271 ayoyi · 91 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,

  2. da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

  3. za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

  4. Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji, “Ina kawo al’umma daga nesa a kanku al’umma ce ta tun dā mai ƙarfin hali, mutane ne da ba ku san harshensu ba, waɗanda ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba.

  5. Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne; dukansu jarumawa ne.

  6. Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku, za su cinye ’ya’yanku maza da mata; za su cinye garkunan tumakinku da na awakinku, za su cinye ’ya’yan inabinku da na ɓaurenku. Da takobi za su hallaka biranenku masu katanga.

  7. “Amma ko a cikin waɗancan kwanaki,” in ji Ubangiji, “ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba.

  8. Sa’an nan annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka saurara, Hananiya! Ubangiji bai aike ka ba, duk da haka ka lallashe wannan al’umma su dogara ga ƙarya.

  9. Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Ina shirin kawar da kai daga fuskar duniya. A wannan shekara za ka mutu, domin ka yi wa’azin tawaye a kan Ubangiji.’ ”

  10. A wata na bakwai na wannan shekara, annabi Hananiya ya mutu.

  11. Sau da sau na aiki bayina annabawa, waɗanda suka ce, ‘Kada ku yi wannan abin ƙyama da na ƙi!’

  12. Amma ba su saurara ko su kasa kunne ba; ba su juye daga muguntarsu ko su daina ƙone turare wa waɗansu alloli ba.

  13. Saboda haka, fushina mai ƙuna ya fāɗo a kan garuruwan Yahuda da kuma titunan Urushalima na kuma mai da su kufai da suke a yau.

  14. Ni ne mutumin da ya ga azaba ta wurin bulalar fushin Ubangiji.

  15. Ya kore ni, ya sa na yi tafiya a cikin duhu maimakon a cikin haske;

  16. ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni sau da sau, dukan yini.

  17. Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa ya kuma karya ƙasusuwana.

  18. Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni da baƙin ciki da kuma wahala.

  19. Ya sa na zauna a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu da jimawa.

  20. Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba; Ya daure ni da sarƙa mai nauyi.

  21. Ko lokacin da nake kira don neman taimako, ba ya jin addu’ata.

  22. Ya tare hanyata da tubula na duwatsu; ya sa hanyata ta karkace.

  23. Kamar beyar da take a laɓe tana jira, kamar zaki a ɓoye,

  24. ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni ya bar ni ba taimako.

  25. Ya ja kwarinsa ya sa in zama abin baratarsa.