Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Judgments

271 ayoyi · 91 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ya harbi zuciyata da kibiyoyin kwarinsa.

  2. Na zama abin dariya ga mutanena duka; suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.

  3. Ya cika ni da kayan ɗaci ya gundure ni da abinci mai ɗaci.

  4. Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa; ya tattake ni cikin ƙura.

  5. An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata.

  6. Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.”

  7. Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai.

  8. Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina.

  9. “Na kuma hana muku ruwan sama tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi. Na sa aka yi ruwan sama a wani gari, sai na hana a yi a wani gari. Wata gona ta sami ruwan sama; wata gona kuma ta bushe.

  10. Mutane suna tangaɗi daga gari zuwa gari suna neman ruwa amma ba su sami isashen ruwan sha ba, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.

  11. “Sau da yawa na ɓata gonakinku da fumfuna da kuma cuta. Fāri suka cinye itatuwanku na inabi da na ɓaure, da na zaitun duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.

  12. To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa.

  13. Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni.

  14. Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin?

  15. Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”

  16. Da Ananiyas ya ji wannan, sai ya fāɗi ya mutu. Sai babban tsoro kuwa ya kama duk waɗanda suka ji abin da ya faru.

  17. Sai samari suka zo gaba, suka naɗe gawarsa, suka fitar da shi suka je suka binne.

  18. Bayan kusan awa uku, sai matarsa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba.

  19. Bitrus ya tambaye ta ya ce, “Gaya mini, kuɗin da yake da Ananiyas kuka sayar da filin ke nan?” Ta ce, “I, haka ne muka sayar.”

  20. Bitrus ya ce mata, “Ta yaya kuka yarda ku gwada Ruhun Ubangiji? Duba! Sawun mutanen da suka binne mijinki suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki zuwa waje ke ma.”

  21. Nan take ta fāɗi a ƙafafunsa ta mutu. Sai samarin suka shigo ciki, suka kuwa same ta matacciya, suka ɗauke ta suka kai ta waje suka binne ta kusa da mijinta.