Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Judgments: Despising the warnings of God

11 ayoyi · 91 fannoni

Ayoyi game da Despising the warnings of God

  1. Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,

  2. da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,

  3. Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,

  4. sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.

  5. “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.

  6. Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,

  7. da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

  8. za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

  9. Sau da sau na aiki bayina annabawa, waɗanda suka ce, ‘Kada ku yi wannan abin ƙyama da na ƙi!’

  10. Amma ba su saurara ko su kasa kunne ba; ba su juye daga muguntarsu ko su daina ƙone turare wa waɗansu alloli ba.

  11. Saboda haka, fushina mai ƙuna ya fāɗo a kan garuruwan Yahuda da kuma titunan Urushalima na kuma mai da su kufai da suke a yau.