Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Judgments: Upon Sennacherib

3 ayoyi · 91 fannoni

Ayoyi game da Upon Sennacherib

  1. A daren nan mala’ikan Ubangiji ya fita ya kashe dakaru dubu ɗari da tamanin da biyu a sansanin Assuriyawa. Da mutane suka farka da safe, sai ga gawawwaki ko’ina.

  2. Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya tā da sansanin ya kuma janye. Ya koma Ninebe ya zauna a can.

  3. Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi.