- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Armies
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Bayan Arameyawa suka ga Isra’ila ta ci su da yaƙi, sai suka sāke tattara kansu.
Hadadezer sarkin Zoba ya aika a kawo Arameyawan da suke ƙetaren Kogin Yuferites. Suka iso Helam a ƙarƙashin shugabancin Shobak, shugaban dukan sojojin Hadadezer.
Dawuda ya tattara mutanen da suke tare da shi, ya naɗa musu komandodi na dubu-dubu, da na ɗari-ɗari.
Dawuda ya sa rundunoni kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Yowab, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Abishai, ɗan’uwan Yowab ɗan Zeruhiya, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Ittai mutumin Gat. Sai sarki ya ce wa rundunonin, “Tabbatacce zan tafi tare da ku.”
Har yanzu yaƙi ya sāke ɓarke tsakanin Filistiyawa da Isra’ila. Sai Dawuda ya gangara tare da mutanensa don su yaƙi Filistiyawa, gajiya ta kama shi.
Ishbi-Benob kuwa, wani daga zuriyar Rafa, wanda nauyin kan māshinsa na tagulla ya yi shekel ɗari uku, wanda yake kuma da sabon māshi, ya ce zai kashe Dawuda.
Amma Abishai ɗan Zeruhiya ya kawo wa Dawuda gudummawa; ya bugi Bafilistin, ya kashe shi. Sa’an nan mutanen Dawuda suka rantse masa suka ce, “Ba za ka ƙara fita tare da mu wurin yaƙi ba, don kada fitilar Isra’ila tă mutu.”
Ana nan, sai aka sāke yin wani yaƙin da Filistiyawa, a Gob. A lokacin Sibbekai mutumin Husha ya kashe Saf, wani daga zuriyar Rafa.
Sai aka sāke yin wani yaƙin da Filistiyawa a Gob, Elhanan ɗan Ya’are-Oregim mutumin Betlehem ya kashe Goliyat mutumin Gat, wanda girmar sandan māshinsa ta yi kama da taɓarya.
Har wa yau a wani yaƙin da aka yi a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu, da kuma yatsotsi shida a kowane ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriya Rafa ne.
Da ya yi wa Isra’ila reni, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwa Dawuda, ya kashe shi.
Waɗannan huɗu zuriyar Rafa ne a Gat, suka kuwa mutu ta hannu Dawuda da mutanensa.
Fushin Ubangiji ya sāke ƙuna a kan Isra’ila, sai ya zuga Dawuda, yana cewa, “Je ka ƙidaya Isra’ila da Yahuda.”
Saboda haka sarki ya ce wa Yowab da komandodin da suke tare da shi, “Tafi cikin dukan kabilan Isra’ila, daga Dan har zuwa Beyersheba, ku ƙidaya mayaƙa don in san yawansu.”
Amma Yowab ya ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya sa mayaƙan su ƙaru sau ɗari fiye da yadda suke, har ranka yă daɗe, sarki yă gani da idonsa. Me ya sa ranka yă daɗe, sarki yake so yă yi abu haka?”
Duk da haka, maganar sarki ya rinjayi Yowab da komandodin soja, sai suka tashi daga gaban sarki, suka tafi su ƙirga mayaƙan Isra’ila.
Bayan suka ƙetare Urdun, sai suka yi sansani kusa da Arower, kudu da garin da yake cikin kwari, sa’an nan suka ratsa ta wajen Gad, suka ci gaba zuwa Yazer.
Suka tafi Gileyad ta yankin Tatim Hodshi, sa’an nan suka tafi Dan Ya’an, suka kuma yi wajen kewaye Sidon.
Sa’an nan suka yi ta wajen kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa da Kan’aniyawa. A ƙarshe, suka ci gaba zuwa Beyersheba a Negeb na Yahuda.
Bayan suka ratsa dukan ƙasashen, a ƙarshe suka koma Urushalima, bayan wata tara da kwana ashirin.
Yowab ya ba wa sarki jimillar yawan mayaƙan. A Isra’ila akwai mutum dubu ɗari takwas da za su iya riƙe takobi. A Yahuda kuwa mutum dubu ɗari biyar.
Aka yi shekaru uku ba a yi yaƙi tsakanin Aram da Isra’ila ba.
Amma a shekara ta uku, Yehoshafat sarkin Yahuda ya gangara don yă ga sarki Isra’ila.
Sarkin Isra’ila ya ce wa shugabanninsa, “Ba ku san cewa Ramot Gileyad namu ne ba, duk da haka ba mu yi kome ba don mu sāke karɓanta daga sarkin Aram?”
Saboda haka ya tambayi Yehoshafat, ya ce, “Za ka tafi tare da ni don in yi yaƙi da Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa wa sarkin Isra’ila, ya ce, “Ni ma kamar ka ne, mutanena kuwa kamar mutanenka, dawakaina kamar dawakanka.”