Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Armies

207 ayoyi · 77 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kwana arba’in cif, Bafilistin nan ya yi ta fitowa kowane safe da kuma kowace yamma.

  2. Yesse ya ce wa ɗansa Dawuda, “Ka ɗauki wannan gasasshen hatsi da waɗannan curin burodi goma, ka kai wa ’yan’uwanka a sansani da sauri.

  3. Ka haɗa da waɗannan cuku guda goma, ka kai wa komandan rundunarsu. Ka ga lafiyar ’yan’uwanka, ka kawo mini labari daga wurinsu.

  4. Suna tare da Shawulu da kuma dukan mutanen Isra’ila a Kwarin Ela, suna can suna yaƙi da Filistiyawa.”

  5. Kashegari da sassafe, Dawuda ya tashi ya bar tumakinsa wa wani yă lura da su, sai ya ɗauki kayansa, ya kama hanya kamar yadda Yesse ya umarce shi. Ya isa sansanin daidai sa’ad da rundunar tana fitowa zuwa bakin dāgā, suna kirarin yaƙi.

  6. Isra’ila da Filistiyawa suka ja dāgā suna fuskantar junansu.

  7. Dawuda ya bar kayansa a wajen wani mai lura da kaya, sai ya ruga zuwa bakin dāgā yă gai da ’yan’uwansa.

  8. Da yana magana da su sai Goliyat, jarumin nan Bafilistin daga Gat ya fito daga rundunar Filistiyawa, ya tā da murya kamar yadda ya saba. Dawuda kuwa ya ji shi.

  9. Da Isra’ilawa suka ga mutumin, sai dukansu suka gudu saboda tsananin tsoro.

  10. Isra’ilawa suka yi ta cewa, “Kun ga yadda wannan mutum yana ta fitowa? Yana fitowa ne don yă kalubalanci Isra’ila. Sarki zai sāka wa mutumin da ya kashe wannan da dukiya mai yawa. Zai kuma ba shi ’yarsa yă aura, yă cire suna mahaifinsa daga biyan kuɗin haraji cikin Isra’ila.”

  11. Dawuda ya tambayi mutanen da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilistin nan, ya kuma cire wannan kunya daga Isra’ila? Wane ne wannan bafilistin marar kaciya da yake kalubalantar rundunar yaƙi na Allah mai rai?”

  12. Sai suka sāke gaya masa abin da suka faɗa cewa, “Ga abin da zai faru da wanda ya kashe shi.”

  13. Da wansa Eliyab, ya ji yana magana da mutanen, sai ransa ya ɓace ƙwarai saboda fushi, sai ya ce wa Dawuda, “Me ka zo yi a nan? Wa kuma ka bar wa ’yan tumakin a jeji? Na san ka da taurinkai, da kuma mugun hali. Ka zo nan ne don ka yi kallon yaƙi kawai.”

  14. Dawuda ya ce, “To, yanzu me na yi? Ba zan ma yi magana ba?”

  15. Sai ya juya wajen wani kuma ya sāke kawo zancen, mutanen kuwa suka amsa masa kamar dā.

  16. Aka ji abin da Dawuda ya ce, aka kuwa gaya wa Shawulu, Shawulu kuma ya aika a kawo shi.

  17. Da Shawulu ya tambayi Dawuda, sai Dawuda ya ce masa, “Kada kowa yă damu saboda wannan Bafilistin. Bawanka zai je yă yi faɗa da shi.”

  18. Shawulu ya ce, “Ba za ka iya yin faɗa da wannan Bafilistin ba, ya daɗe yana yaƙi, ya yi yaƙi tun yana saurayi. Ga shi kuwa kai ɗan yaro ne kawai.”

  19. Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Bawanka yana kiwon tumakin mahaifinsa. Sa’ad da zaki ko beyar ta zo ta kama tunkiya, ta tafi da ita.

  20. Nakan bi ta a baya in buga ta in kuma ƙwato tunkiyar daga bakinta. In kuma ta taso mini, nakan cafke ta a gashinta in buga ta in kashe.

  21. Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai.

  22. Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Je ka, Ubangiji yă kasance tare da kai.”

  23. Sai Shawulu ya kawo kayan yaƙinsa ya sa wa Dawuda. Ya sa masa hular kwanon da aka yi da tagulla a kansa, ya kuma sa masa rigar ƙarfensa.

  24. Dawuda ya ɗaura māshin Shawulu a sulken, ya yi ƙoƙari yă zaga, sai ya ji ba zai iya ba saboda bai saba ba. Ya cewa Shawulu, “Ba zan iya tafiya da waɗannan ba, domin ban saba ba.” Don haka ya tuɓe su.

  25. Sai ya ɗauki sandansa, ya zaɓi duwatsu guda biyar masu sulɓi daga cikin rafi, ya sa su a ’yar jakarsa ta makiyaya; ya kuma ɗauki majajjawarsa, ya tafi, yă fuskanci Bafilistin.