Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Armies

207 ayoyi · 77 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ana ciki haka, sai Bafilistin nan shi ma ya fita yana gusowa zuwa wurin Dawuda. Mai riƙe masa garkuwar yaƙi kuwa yana tafe a gabansa.

  2. Bafilistin ya dubi Dawuda daga sama har ƙasa, ya gan dai ɗan yaro ne kawai, kyakkyawa kuma mai ƙoshin lafiya, sai ya rena shi.

  3. Ya ce masa, “Kana tsammani ni kare ne da za ka zo mini da sanda?” Sai ya la’anci Dawuda da sunayen allolin Filistiyawa.

  4. Ya ce, “Zo nan, ni kuwa zan ba da naman jikinka ga tsuntsayen sama da namun jeji su ci.”

  5. Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena.

  6. Yau nan, Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan kuwa kashe ka, in datse kanka. Yau, zan ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namun jeji, da haka duniya za tă sani lalle akwai Allah a cikin Isra’ila.

  7. Duk waɗanda suka taru a nan za su san cewa ba da māshi ko takobi ne Ubangiji yake ceto ba, gama yaƙin nan na Ubangiji ne, shi kuwa zai bashe ku duka a hannuwanmu.”

  8. Yayinda Bafilistin yana matsowa kusa domin yă fāɗa wa Dawuda, sai Dawuda ya ruga a guje zuwa bakin dāgā don yă same shi.

  9. Ya sa hannu a jakarsa ya ɗauki dutse, ya sa cikin majajjawa ya wurga, dutsen kuwa ya bugi Bafilistin a goshi, dutsen ya shiga cikin goshinsa, sai Bafilistin ya fāɗi rubda ciki.

  10. Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara a kan Bafilistin. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.

  11. Dawuda ya ruga ya tsaya a bisan Bafilistin, ya zare takobin Bafilistin daga kubensa, ya datse masa kai da shi. Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka juya suka gudu.

  12. Mutanen Isra’ila da na Yahuda suka rugo gaba da babbar murya, suka fafari Filistiyawa har zuwa mashigin Gat da kuma ƙofofin Ekron. Gawawwakin Filistiyawa suka bazu a hanyar Sha’arayim zuwa Gat da kuma Ekron.

  13. Da Isra’ilawa suka komo daga bin Filistiyawa sai suka washe sansanin Filistiyawa.

  14. Dawuda ya bar Gat, ya tsere zuwa kogon Adullam. Da ’yan’uwansa da kuma iyalan mahaifinsa suka ji labari, sai suka tafi can wurinsa.

  15. Dukan mutanen da suke cikin wahala, da waɗanda ake binsu bashi, da masu damuwoyi, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Yawansu ya kai ɗari huɗu.

  16. Sai Shawulu ya ce wa mai ɗauka masa makami, “Ka zare takobinka ka soke ni, kada waɗannan marasa kaciya su zo su ci mini mutunci, su kashe ni.” Amma mai ɗaukan makaman bai yarda ba don ya ji tsoro sosai. Sai Shawulu ya zāre takobinsa ya soki kansa.

  17. Da mai ɗaukar makamai ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya zāre takobinsa ya soki kansa ya mutu.

  18. Shawulu da yaransa uku da mai ɗaukar makamansa da dukan mutanensa suka mutu a rana ɗaya.

  19. Ana cikin haka, Abner ɗan Ner, komandan sojojin Shawulu, ya ɗauki Ish-Boshet ɗan Shawulu ya kawo shi Mahanayim.

  20. Ya naɗa shi sarkin Gileyad, da na Ashuri, da na Yezireyel, da a kan Efraim, da Benyamin, da kuma na dukan Isra’ila.

  21. Ish-Boshet ɗan Shawulu yana da shekaru arba’in sa’ad da ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi sarauta shekara biyu. Amma fa, gidan Yahuda, suka bi Dawuda.

  22. Sa’an nan Abner ya ce wa Yowab, “Bari mu bar waɗansu samari su tashi su yi faɗa hannu da hannu a gabanmu.” Yowab ya ce, “To, su tashi.”

  23. Saboda haka samarin suka tashi aka ƙidaya su, mutum sha biyu wajen Benyamin da Ish-Boshet ɗan Shawulu, sha biyu kuma wajen Dawuda.

  24. Sa’an nan kowannensu ya kama abokin gābansa a kā ya soki da wuƙa a jiki, sai duka suka fāɗi a ƙasa. Saboda haka ne ake kiran wannan wuri Helkat Hazzurim a Gibeyon.

  25. Faɗan ya yi zafi a ranar ƙwarai, mutanen Dawuda suka ci mutanen Abner da na Isra’ila.