Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Armies

207 ayoyi · 77 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A shekara ta bakwai sai Yehohiyada ya aika a kira komandodin sojoji ɗari-ɗari, da Keretawa, da matsara, ya sa aka kawo masa su a haikalin Ubangiji. Ya ƙulla yarjejjeniya da rantsuwa da su a haikalin Ubangiji, sa’an nan ya nuna musu ɗan sarki.

  2. Ya umarce su cewa, “Ga abin da za ku yi sa’ad da kuka zo aiki a Asabbaci, ku raba kanku kashi uku. Kashi ɗaya za su yi gadin gidan sarki,

  3. kashi ɗaya za su yi gadin Ƙofar Sur, kashi ɗaya kuma za su yi gadin ƙofar da take bayan ’yan gadin fada. Dukan waɗannan ƙungiyoyi uku za su yi gadin fadan,

  4. ku kuma da kuke a sauran ƙungiyoyi biyu da kun saba hutu a Asabbaci, duk za ku yi gadin haikali don sarki.

  5. Ku tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makaminsa a hannu. Duk wanda ya kusace ku, ku kashe shi. Ku manne wa sarki duk inda ya tafi.”

  6. Komandodin sojoji suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowa ya ɗauki mutanensa, waɗanda za su kama aiki Asabbaci da waɗanda za su kama hutun Asabbaci, suka zo wurin Yehohiyada firist.

  7. Sai ya ba komandodin māsu da garkuwoyi da dā suke na Dawuda, waɗanda suke a cikin haikalin Ubangiji.

  8. Matsaran kuma kowa da makaminsa a hannu, suka tsaya kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikalin.

  9. Sai Yehohiyada ya fito da ɗan sarki ya sa masa rawani a kā; ya ba shi shafin alkawari, ya kuma furta shi sarki. Suka shafe shi da mai, mutane kuma suka yi ta tafi suka ihu, suna cewa, “Ran sarki yă daɗe.”

  10. Jagoran dogarawan sarkin Assuriya ya ce musu, “Ku ce wa Hezekiya, “ ‘Ga abin da babban sarkin Assuriya ya ce, da wa kake taƙama?

  11. Ka ce kana da dabara da ƙarfin soji, amma bagu kawai kake yi. Da wa ka dogara har da za ka yi mini tawaye?

  12. Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi.

  13. Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram-Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba.

  14. Suka yi hayar kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi dubu talatin da biyu, da kuma sarkin Ma’aka tare da mayaƙansa, waɗanda suka zo suka kafa sansani kusa da Medeba, yayinda Ammonawa suka tattaru daga garuruwansu suka fita yaƙi.

  15. Sai Asa ya ɗauki azurfa da zinariya daga ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma na fadansa ya aika wa Ben-Hadad sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus.

  16. Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakani na da kai kamar yadda ya kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Dubi ina aika maka azurfa da zinariya. Yanzu ka yanke yarjejjeniya da Ba’asha sarkin Isra’ila domin yă janye daga gare ni.”

  17. Ben-Hadad ya yarda da Sarki Asa ya kuma aika da manyan hafsoshin mayaƙansa a kan garuruwan Isra’ila. Suka ci Iyon, Dan, Abel-Mayim da kuma dukan biranen ajiya na Naftali.

  18. Da Ba’asha ya ji wannan, ya daina ginin Rama ya yashe aikinsa.

  19. Sa’an nan Sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuda, suka kuma kwashe duwatsu da katako daga Rama waɗanda Ba’asha yake amfani da su. Da su ne Asa ya gina Geba da Mizfa.

  20. A lokacin Hanani mai duba ya zo wurin Asa sarkin Yahuda ya ce masa, “Don ka dogara ga sarkin Aram, ba kuwa ga Ubangiji Allahnka ba ne mayaƙan sarkin Aram sun kuɓuce daga hannunka.

  21. Ai, Kushawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da kekunan yaƙi da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, ya kuwa ba da su cikin hannunka.

  22. Gama gaban Ubangiji yana ko’ina a duniya don yă ƙarfafa waɗanda zukatansu suke binsa cikin aminci. Ka yi wauta, daga yanzu nan gaba za ka yi ta yaƙi.”

  23. Yehoshafat ya yi ta ƙaruwa a ƙarfi; ya gina katanga da biranen ajiya a Yahuda

  24. da kuma tanade-tanade masu yawa a garuruwan Yahuda. Ya kuma ajiye gogaggu mayaƙa a Urushalima.

  25. Ɗaukar da aka yi musu bisa ga iyalai yana kamar haka. Daga Yahuda, shugaban ƙungiya 1,000. Adna ne shugaba, tare da jarumawa 300,000;