Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Armies: Who were exempt from service in

9 ayoyi · 77 fannoni

Ayoyi game da Who were exempt from service in

  1. Ba a dai ƙidaya zuriyar Lawi tare da saura kabilan ba.

  2. Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa,

  3. “Ka tabbatar ba ka ƙidaya mutanen Lawi ko kuma ka haɗe su tare a ƙidayan sauran Isra’ilawa ba.

  4. A maimakon haka sai ka naɗa Lawiyawa su lura da tabanakul Shaida, wato, kan dukan kayayyaki da kuma kome da yake na wuri mai tsarki. Za su ɗauko tabanakul da dukan kayayyakinsa; za su lura da shi, su kasance kewaye da shi.

  5. Hafsoshi za su ce wa mayaƙa, “Ko akwai wanda ya gina sabon gida bai kuma buɗe shi ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă buɗe shi.

  6. Ko akwai wani da ya shuka inabi, bai kuwa fara jin daɗinsa ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă ji daɗinsa.

  7. Ko akwai wani da aka yi masa alkawarin mata, bai kuwa aure ta ko ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă aure ta.”

  8. Sa’an nan hafsoshin za su ƙara da cewa, “Ko akwai wani da yake tsoro, ko ya karai? Bari yă tafi gida don kada ’yan’uwansa su karai su ma.”

  9. Sa’ad da hafsoshin suka gama magana da mayaƙan, sai su naɗa komandodi a kansu.