Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Armies: Determine royal succession

12 ayoyi · 77 fannoni

Ayoyi game da Determine royal succession

  1. Ana cikin haka, Abner ɗan Ner, komandan sojojin Shawulu, ya ɗauki Ish-Boshet ɗan Shawulu ya kawo shi Mahanayim.

  2. Ya naɗa shi sarkin Gileyad, da na Ashuri, da na Yezireyel, da a kan Efraim, da Benyamin, da kuma na dukan Isra’ila.

  3. Ish-Boshet ɗan Shawulu yana da shekaru arba’in sa’ad da ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi sarauta shekara biyu. Amma fa, gidan Yahuda, suka bi Dawuda.

  4. A shekara ta bakwai sai Yehohiyada ya aika a kira komandodin sojoji ɗari-ɗari, da Keretawa, da matsara, ya sa aka kawo masa su a haikalin Ubangiji. Ya ƙulla yarjejjeniya da rantsuwa da su a haikalin Ubangiji, sa’an nan ya nuna musu ɗan sarki.

  5. Ya umarce su cewa, “Ga abin da za ku yi sa’ad da kuka zo aiki a Asabbaci, ku raba kanku kashi uku. Kashi ɗaya za su yi gadin gidan sarki,

  6. kashi ɗaya za su yi gadin Ƙofar Sur, kashi ɗaya kuma za su yi gadin ƙofar da take bayan ’yan gadin fada. Dukan waɗannan ƙungiyoyi uku za su yi gadin fadan,

  7. ku kuma da kuke a sauran ƙungiyoyi biyu da kun saba hutu a Asabbaci, duk za ku yi gadin haikali don sarki.

  8. Ku tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makaminsa a hannu. Duk wanda ya kusace ku, ku kashe shi. Ku manne wa sarki duk inda ya tafi.”

  9. Komandodin sojoji suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowa ya ɗauki mutanensa, waɗanda za su kama aiki Asabbaci da waɗanda za su kama hutun Asabbaci, suka zo wurin Yehohiyada firist.

  10. Sai ya ba komandodin māsu da garkuwoyi da dā suke na Dawuda, waɗanda suke a cikin haikalin Ubangiji.

  11. Matsaran kuma kowa da makaminsa a hannu, suka tsaya kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikalin.

  12. Sai Yehohiyada ya fito da ɗan sarki ya sa masa rawani a kā; ya ba shi shafin alkawari, ya kuma furta shi sarki. Suka shafe shi da mai, mutane kuma suka yi ta tafi suka ihu, suna cewa, “Ran sarki yă daɗe.”