Tsallake zuwa abun ciki

the giant in Gath

7 ayoyi · 5 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci the giant in Gath

  1. Ishbi-Benob kuwa, wani daga zuriyar Rafa, wanda nauyin kan māshinsa na tagulla ya yi shekel ɗari uku, wanda yake kuma da sabon māshi, ya ce zai kashe Dawuda.

  2. Ana nan, sai aka sāke yin wani yaƙin da Filistiyawa, a Gob. A lokacin Sibbekai mutumin Husha ya kashe Saf, wani daga zuriyar Rafa.

  3. Har wa yau a wani yaƙin da aka yi a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu, da kuma yatsotsi shida a kowane ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriya Rafa ne.

  4. Waɗannan huɗu zuriyar Rafa ne a Gat, suka kuwa mutu ta hannu Dawuda da mutanensa.

  5. Ana nan, sai yaƙi ya ɓarke a Gezer tsakanin Isra’ila da Filistiyawa. Sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin zuriyar Refahiyawa, ta haka kuma aka ci Filistiyawa da yaƙi.

  6. Aka sāke yin wani yaƙin kuma, wanda ya faru a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu da kuma yatsotsi shida a kowace ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriyar Rafa ce.

  7. Waɗannan su ne zuriyar Rafa a Gat, Dawuda da mutanensa sun kashe su.