Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ishaya 31:5kusan 713 K.H.

    Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima; zai kāre ta ya kuma fanshe ta, zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.”

  2. Ishaya 31:6kusan 713 K.H.

    Ku dawo gare shi ku da kuka yi masa babban tayarwa, ya Isra’ilawa.

  3. Ishaya 31:7kusan 713 K.H.

    Gama a wannan rana kowannenku zai ƙi gumakan azurfa da zinariya da hannuwanku masu zunubi suka yi.

  4. Ishaya 31:8kusan 713 K.H.

    “Za a karkashe Assuriyawa da takobin da ba na yin mutum ba; takobi, da ba na yin mutum ba, zai cinye. Za su gudu daga takobi za a kuma sa samarinsu aikin dole.

  5. Ishaya 31:9kusan 713 K.H.

    Kagararsu za tă fāɗi saboda razana; da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,” in ji Ubangiji, wanda wutarsa tana a Sihiyona, wanda matoyarsa tana a Urushalima.

  6. Ishaya 32:1kusan 713 K.H.

    Duba, sarki zai yi mulki cikin adalci masu mulki kuma su yi mulki da adalci.

  7. Ishaya 32:2kusan 713 K.H.

    Kowane mutum zai zama kamar wurin fakewa daga iska mafaka kuma daga hadari, kamar rafuffukan ruwa a hamada da kuma inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.

  8. Ishaya 32:3kusan 713 K.H.

    Sa’an nan idanun waɗanda suka gani ba za su ƙara rufewa ba, kunnuwan waɗanda suka ji kuma za su saurara.

  9. Ishaya 32:4kusan 713 K.H.

    Zuciya marasa haƙuri za su sani su kuma fahimta, harshen masu ana’ana kuma zai sāke su yi magana sosai.

  10. Ishaya 32:5kusan 713 K.H.

    Ba za a ƙara ce da wawa mai girma ba ko kuwa a ɗaukaka mazambaci.

  11. Ishaya 32:6kusan 713 K.H.

    Gama wawa maganar wauta yakan yi, zuciyarsa ta cika da mugunta, yana aikata abubuwan rashin sanin Allah yana baza kurakurai game da Ubangiji; yana barin mayunwata da yunwa ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha.

  12. Ishaya 32:7kusan 713 K.H.

    Matakan mazambaci mugaye ne, yana ƙulla mugayen shirye-shirye don yă hallaka talakawa da ƙarairayi, ko sa’ad da roƙon mai bukata da gaskiya ne.

  13. Ishaya 32:8kusan 713 K.H.

    Amma mutumin kirki kan yi shirye-shirye masu kirki, kuma yakan tsaya a kan ayyukan kirki.

  14. Ishaya 32:9kusan 713 K.H.

    Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ku tashi ku saurare ni; ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya, ku ji abin da zan faɗa!

  15. Ishaya 32:10kusan 713 K.H.

    Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki; girbin ’ya’yan inabi zai kāsa, girbin ’ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba.

  16. Ishaya 32:11kusan 713 K.H.

    Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi, ku sha wahala, ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya! Ku tuɓe rigunanku, ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.

  17. Ishaya 32:12kusan 713 K.H.

    Ku bugi ƙirjinku don gonaki masu kyau don ’ya’yan inabi

  18. Ishaya 32:13kusan 713 K.H.

    da kuma don ƙasar mutanena, da ƙasar da ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suka yi girma, I, ku yi kuka saboda dukan gidajen da dā ake biki da kuma domin wannan birnin da dā ake murna a ciki.

  19. Ishaya 32:14kusan 713 K.H.

    Za a ƙyale kagarar, a gudu a bar birnin da dā ake hayaniya; mafaka da hasumiyar tsaro za su zama kango har abada, jin daɗin jakuna, makiyaya don garkuna,

  20. Ishaya 32:15kusan 713 K.H.

    sai an zubo Ruhu a kanmu daga sama, hamada kuma ta zama ƙasar mai taƙi, gona mai taƙi kuma ta zama kamar kurmi.

  21. Ishaya 32:16kusan 713 K.H.

    Aikin gaskiya zai zauna a hamada adalci kuma zai zauna a ƙasa mai taƙi.

  22. Ishaya 32:17kusan 713 K.H.

    Aikin adalci zai zama salama; tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.

  23. Ishaya 32:18kusan 713 K.H.

    Mutanena za su zauna lafiya a wuraren salama, a gidaje masu kāriya, a wuraren hutun da babu fitina.

  24. Ishaya 32:19kusan 713 K.H.

    Ko da yake ƙanƙara za tă fāɗo a jeji, a kuma rurrushe birni gaba ɗaya,

  25. Ishaya 32:20kusan 713 K.H.

    zai zama muku da albarka, ku da kuke shuki iri kusa da kowane rafi, kuna kuma barin lafiyayyiyar makiyaya domin shanu da jakunanku.