Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 30–62

The Early Church

Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.

1,007 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. In kuma akwai wani abu har yanzu da kuke so ku kawo, dole a daidaita shi a majalisa.

  2. Yadda yake a yanzu, muna a hatsarin amsa zargin ta da hargitsi saboda abin da ya faru yau. Da yake ba za mu iya ba da dalilin da ya sa aka yi wannan hargitsi ba.”

  3. Bayan da ya faɗi haka, sai ya sallami taron.

  4. Sa’ad da hayaniyar ta kwanta, sai Bulus ya aika a kira almajiran, kuma bayan ya ƙarfafa su, sai ya yi bankwana ya tafi Makidoniya.

  5. Ya ratsa wurin yana ƙarfafa mutanen da kalmomi masu yawa, a ƙarshe kuma ya kai Giris,

  6. inda ya zauna wata uku. Da yake Yahudawa sun ƙulla masa makirci, a lokacin da yake shirin tashi cikin jirgin ruwa zuwa Suriya, sai ya yanka shawara yă koma ta Makidoniya.

  7. Sai Sofater ɗan Fairrus daga Bereya, Aristarkus da Sekundus daga Tessalonika, Gayus daga Derbe, Timoti ma, da Tikikus da Turofimus daga lardin Asiya suka tafi tare da shi.

  8. Waɗannan mutane suka sha gaba suka kuma jira mu a Toruwas.

  9. Amma muka tashi daga Filibbi a jirgin ruwa bayan Bikin Burodi Marar Yisti bayan kuma kwana biyar muka sadu da sauran a Toruwas, inda muka zauna kwana bakwai.

  10. A ranar farko ta mako muka taru wuri ɗaya don gutsuttsura burodi. Bulus ya yi wa mutane magana, don yana niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta yin magana har tsakar dare.

  11. Akwai fitilu da yawa a ɗakin gidan saman da muka taru.

  12. Akwai wani saurayi zaune a taga mai suna Yitikus, wanda barci mai nauyi ya ɗauke shi yayinda Bulus yake ta tsawaita magana. Sa’ad da yake barci, sai ya fāɗi daga gidan sama a hawa ta uku aka kuma ɗauke shi matacce.

  13. Sai Bulus ya sauka, ya miƙe a kan saurayin ya rungume shi ya ce, “Kada ku damu, yana da rai!”

  14. Sai ya koma ɗakin da yake a gidan sama, ya gutsuttsura burodi ya kuma ci. Bayan ya yi magana har gari ya waye, sai ya tafi.

  15. Mutanen suka ɗauki saurayin da rai zuwa gida suka kuma ta’azantu ƙwarai da gaske.

  16. Mu kuwa muka ci gaba zuwa jirgin ruwan muka tashi muka nufi Assos inda za mu ɗauki Bulus. Ya yi wannan shirin don zai tafi can da ƙafa.

  17. Da ya same mu a Assos, sai muka ɗauke shi a jirgin ruwan muka zo Mitilen.

  18. Kashegari muka tashi cikin jirgin ruwa daga can muka zo gefen Kiyos. Kwana ɗaya bayan wannan, sai muka ƙetare zuwa Samos, kashegari kuma muka iso Miletus.

  19. Bulus ya yanke shawara yă wuce Afisa a jirgin ruwa don kada yă ɓata lokaci a lardin Asiya, gama yana sauri yă kai Urushalima, in ya yiwu ma, a ranar Fentekos.

  20. Daga Miletus, Bulus ya aika zuwa Afisa a kira dattawan ikkilisiya.

  21. Da suka iso, sai ya ce musu, “Kun san irin zaman da na yi tun lokacin da na zauna da ku, daga ranar farkon da na zo cikin lardin Asiya.

  22. Na bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali’u har da hawaye, da gwagwarmaya iri-irin da na sha game da makircin Yahudawa.

  23. Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku wa’azi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida.

  24. Na yi shela ga Yahudawa da Hellenawa cewa dole su juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu.

  25. “Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba.