Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 30–62

The Early Church

Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.

1,007 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Sai duk suka juya kan Sostenes shugaban majami’a suka yi masa dūka a gaban kotun. Amma Galliyo ko yă kula.

  2. Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korint na ’yan kwanaki. Sa’an nan ya bar ’yan’uwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi.

  3. Suka isa Afisa, inda Bulus ya bar Firiskila da Akwila. Shi kansa ya shiga majami’a ya kuma yi muhawwara da Yahudawa.

  4. Sa’ad da suka roƙe shi ya ƙara ’yan kwanaki da su, bai yarda ba.

  5. Amma da yake barin wurin, ya yi alkawari cewa, “Zan dawo in Allah ya yarda.” Sa’an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.

  6. Sa’ad da ya sauka a Kaisariya, sai ya haura ya gai da ikkilisiya sa’an nan ya gangara zuwa Antiyok.

  7. Bayan ya yi ’yan kwanaki a Antiyok, Bulus ya tashi daga can ya zaga ko’ina a yankin Galatiya da Firjiya, yana ƙarfafa dukan almajirai.

  8. Ana cikin haka sai wani mutumin Yahuda mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi.

  9. An horar da shi a hanyar Ubangiji, ya kuma himma ƙwarai a magana, ya kuma yi koyarwa game da Yesu, daidai, ko da yake baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani.

  10. Sai ya fara magana gabagadi a majami’a. Sa’ad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai.

  11. Sa’ad da Afollos ya so ya tafi Akayya, sai ’yan’uwa suka ƙarfafa shi suka kuma rubuta wa almajiran da suke can da su marabce shi. Da isowarsa, ya zama da taimako ƙwarai ga waɗanda ta wurin alheri suka gaskata.

  12. Gama da ƙwazo ya ƙaryata Yahudawa a muhawwara a fili, yana tabbatar daga Nassosi cewa Yesu shi ne Kiristi.

  13. Lokacin da Afollos yake a Korint, Bulus ya bi hanyar da ta ratsa ta Asiya ya zo Afisa. A can ya sadu da waɗansu almajirai,

  14. sai ya tambaye, su ya ce, “Kun karɓi Ruhu Mai Tsarki sa’ad da kuka gaskata?” Suka amsa suka ce, “A’a, ba mu ma san akwai Ruhu Mai Tsarki ba.”

  15. Saboda haka Bulus ya yi tambaya ya ce, “To, wace baftisma aka yi muku?” Suka ce, “Baftismar Yohanna.”

  16. Bulus ya ce, “Ai, baftismar Yohanna, baftisma ce ta tuba. Ya ce wa mutane su gaskata a wani wanda yake zuwa bayansa, wato, Yesu.”

  17. Da ji wannan, sai aka yi musu baftisma a cikin sunan Ubangiji Yesu.

  18. Da Bulus ya ɗibiya musu hannuwansa, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka musu, suka kuwa yi magana da harsuna, suka kuma yi annabci.

  19. Mutane kuwa su wajen mutum goma sha biyu ne.

  20. Bulus ya shiga majami’a ya yi magana gabagadi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah.

  21. Amma waɗansunsu suka taurara; suka ƙi su gaskata kuma a gaban jama’a suka yi baƙar magana game da Hanyar. Bulus kuwa ya bar su. Ya tafi tare da almajirai ya dinga tattaunawa da su kullum a babban ɗakin jawabi na Tirannus.

  22. Wannan ya ci gaba har shekara biyu, sai da ya sa dukan Yahudawa da Hellenawa da suke zaune a lardin Asiya suka ji maganar Ubangiji.

  23. Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus,

  24. har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su.

  25. Waɗansu Yahudawa masu yawo gari-gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa’azi, na umarce ku, ku fito.”