- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 17:1kusan 53 M.
Da suka bi ta Amfifolis da Afolloniya, sai suka isa Tessalonika, inda akwai majami’ar Yahudawa.
- Ayyukan Manzanni 17:2kusan 53 M.
Kamar yadda ya saba, Bulus ya shiga majami’ar, ranakun Asabbaci uku ya yi ta yin muhawwara da su daga cikin Nassosi,
- Ayyukan Manzanni 17:3kusan 53 M.
yana musu bayani da tabbatarwa cewa dole Kiristi ya sha wahala ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Wannan Yesu da nake sanar muku shi ne Kiristi.”
- Ayyukan Manzanni 17:4kusan 53 M.
Waɗansu Yahudawa suka amince suka kuma bi Bulus da Sila, haka ma Hellenawa da yawa masu tsoron Allah da kuma manyan mata ba kaɗan ba.
- Ayyukan Manzanni 17:5kusan 53 M.
Amma Yahudawa suka yi kishi; saboda haka suka tattara ’yan iska daga kasuwa, suka shirya wata ƙungiya, suka tā da tarzoma a birni. Suka ruga zuwa gidan Yason suna neman Bulus da Sila don su kawo su a gaban taron.
- Ayyukan Manzanni 17:6kusan 53 M.
Amma da ba su same su ba, sai suka ja Yason da waɗansu ’yan’uwa zuwa gaban mahukuntan birnin, suna ihu suna cewa, “Waɗannan mutanen da suke tā da fitina ko’ina a duniya sun iso nan,
- Ayyukan Manzanni 17:7kusan 53 M.
Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.”
- Ayyukan Manzanni 17:8kusan 53 M.
Da suka ji haka, sai hankalin taron da na mahukuntan birnin ya tashi.
- Ayyukan Manzanni 17:9kusan 53 M.
Sai suka sa Yason da sauran su biya kuɗin saki sa’an nan suka sallame su.
- Ayyukan Manzanni 17:10kusan 53 M.
Da dare ya yi, sai ’yan’uwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Bereya. Da suka isa can, sai suka shiga majami’ar Yahudawa.
- Ayyukan Manzanni 17:11kusan 53 M.
Bereyawa kuwa sun fi Tessalonikawa hankali, gama sun karɓi saƙon da marmari ƙwarai, suka kuma yi ta yin bincike Nassosi kowace rana su ga ko abin da Bulus ya faɗa gaskiya ne.
- Ayyukan Manzanni 17:12kusan 53 M.
Yahudawa da yawa suka gaskata, haka ma waɗansu manyan matan Hellenawa da kuma mazan Hellenawa da yawa.
- Ayyukan Manzanni 17:13kusan 53 M.
Da Yahudawan da suke a Tessalonika suka ji cewa Bulus yana wa’azin maganar Allah a Bereya, sai suka je can ma, suna zuga taro suna kuma tā da hankalinsu.
- Ayyukan Manzanni 17:14kusan 53 M.
Nan da nan ’yan’uwa suka sa Bulus yă tafi bakin teku, amma Sila da Timoti suka dakata a Bereya.
- Ayyukan Manzanni 17:15kusan 53 M.
Mutanen da suka raka Bulus kuwa suka kawo shi Atens sa’an nan suka dawo da umarnai wa Sila da Timoti cewa su zo wurinsa da gaggawa.
- Ayyukan Manzanni 17:16kusan 53 M.
Yayinda Bulus yake jiransu a Atens, ya damu ƙwarai da ya ga birnin cike da gumaka.
- Ayyukan Manzanni 17:17kusan 53 M.
Saboda haka ya yi ta muhawwara a majami’a da Yahudawa da kuma Hellenawa masu tsoron Allah, haka kuma da waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa.
- Ayyukan Manzanni 17:18kusan 53 M.
Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana wa’azin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana wa’azin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu.
- Ayyukan Manzanni 17:19kusan 53 M.
Sai suka ɗauke shi suka kawo shi wurin taron Areyofagus, inda suka ce masa, “Ko za mu san mene ne sabon koyarwan nan ya ƙunsa da kake yi?
- Ayyukan Manzanni 17:20kusan 53 M.
Kana kawo mana ra’ayoyin da suke baƙo a gare mu, kuma muna so mu san mene ne suke nufi.”
- Ayyukan Manzanni 17:21kusan 53 M.
(Duk Atenawa da baƙin da suke zama a can suna zaman kashe wando ne kawai kuma ba abin da suke yi sai dai taɗi da kuma jin sababbin ra’ayoyi.)
- Ayyukan Manzanni 17:22kusan 53 M.
Sai Bulus ya miƙe tsaye a tsakiyar taron Areyofagus ya ce, “Ya ku mutanen Atens! Na dai lura cewa ta kowace hanya ku masu addini ne ƙwarai.
- Ayyukan Manzanni 17:23kusan 53 M.
Gama sa’ad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu, Ga Allahn da ba a sani ba. To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku.
- Ayyukan Manzanni 17:24kusan 53 M.
“Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa.
- Ayyukan Manzanni 17:25kusan 53 M.
Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome.