Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 30–62

The Early Church

Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.

1,007 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Yahuda da Sila, waɗanda su kansu annabawa ne, suka yi magana sosai don su gina su kuma ƙarfafa ’yan’uwa.

  2. Bayan suka yi ’yan kwanaki a can, sai ’yan’uwa suka sallame su da albarkar salama su dawo wurin waɗanda suka aike su.

  3. Notwithstanding it pleased Silas to abide there still.

  4. Amma Bulus da Barnabas kuwa suka dakata a Antiyok, inda su da waɗansu da yawa suka yi koyarwa suka kuma yi wa’azin maganar Ubangiji.

  5. Bayan ’yan kwanaki sai Bulus ya ce wa Barnabas, “Mu koma mu ziyarci ’yan’uwa a duk garuruwan da muka yi wa’azin bisharar Ubangiji mu ga yadda suke.”

  6. Barnabas ya so Yohanna, wanda ake kira Markus ya tafi tare da su,

  7. amma Bulus bai ga ya kyautu ya tafi da shi ba, domin ya yashe su a Famfiliya bai kuwa ci gaba tare da su a aikin ba.

  8. Suka sami saɓanin ra’ayi tsakaninsu har suka rabu. Barnabas ya ɗauki Markus suka shiga jirgin ruwa zuwa Saifurus,

  9. amma Bulus ya zaɓi Sila suka kuwa tashi, bayan ’yan’uwa suka danƙa su ga alherin Ubangiji.

  10. Ya ratsa ta Suriya da Silisiya, yana ƙarfafa ikkilisiyoyi.

  11. Bulus ya kai Derbe sa’an nan kuma zuwa Listira, inda wani almajiri mai suna Timoti yake da zama, wanda mahaifiyarsa mutuniyar Yahuda ce kuma mai bi ce, amma mahaifinsa mutumin Hellenawa ne.

  12. ’Yan’uwa a Listira da Ikoniyum sun yi magana mai kyau ƙwarai a kansa.

  13. Bulus ya so ya ɗauke shi a tafiyar, saboda haka ya yi masa kaciya, domin Yahudawan da suke da zama a wurin, don duk sun san cewa mahaifinsa mutumin Hellenawa ne.

  14. Yayinda suke tafiya daga gari zuwa gari, suka dinga ba da shawarwarin da manzanni da dattawa a Urushalima suka zartar domin mutane su kiyaye.

  15. Saboda haka ikkilisiyoyi suka ginu cikin bangaskiya suka kuma yi girma suka yi ta ƙaruwa kowace rana.

  16. Bulus da abokan tafiyarsa suka zazzaga dukan yankin Firjiya da Galatiya, don Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin wa’azi a lardin Asiya.

  17. Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba.

  18. Saboda haka suka ratsa Misiya suka zo Toruwas.

  19. Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.”

  20. Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu wa’azin bishara.

  21. Daga Toruwas muka tashi zuwa teku muka kuma shiga jirgin ruwa muka miƙe kai tsaye zuwa Samotiras, kashegari kuma muka nufi Neyafolis.

  22. Daga can muka tafi Filibbi, wata babbar alkaryar Roma wadda kuma take babban birni a gundumar Makidoniya. Muka zauna a can kwanaki masu yawa.

  23. A Asabbaci, muka fita ƙofar birnin zuwa bakin kogi, inda muke tsammani za mu sami wurin yin addu’a. Muka zauna muka fara yin wa matan da suka taru a can magana.

  24. Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yadunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus.

  25. Da aka yi mata baftisma tare da iyalin gidanta, sai ta gayyace mu zuwa gidanta. Ta ce, “In kun amince ni mai bi ce cikin Ubangiji, sai ku zo ku sauka a gidana.” Sai ta kuwa rinjaye mu.