- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 15:7kusan 51 M.
Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata.
- Ayyukan Manzanni 15:8kusan 51 M.
Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.
- Ayyukan Manzanni 15:9kusan 51 M.
Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya.
- Ayyukan Manzanni 15:10kusan 51 M.
To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba?
- Ayyukan Manzanni 15:11kusan 51 M.
A’a! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”
- Ayyukan Manzanni 15:12kusan 51 M.
Sai duk taron suka yi tsit yayinda suke sauraron Barnabas da Bulus suna ba da labari game da ayyuka da kuma abubuwan banmamakin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurinsu.
- Ayyukan Manzanni 15:13kusan 51 M.
Da suka gama, sai Yaƙub ya yi magana ya ce, “’Yan’uwa, ku saurare ni.
- Ayyukan Manzanni 15:14kusan 51 M.
Siman ya bayyana mana yadda Allah da farko ya nuna damuwarsa ta wurin ɗaukan mutane daga cikin Al’ummai su zama nasa.
- Ayyukan Manzanni 15:15kusan 51 M.
Kalmomin annabawa sun yi daidai da wannan, kamar yadda yake a rubuce cewa,
- Ayyukan Manzanni 15:16kusan 51 M.
“ ‘Bayan wannan zan koma in kuma sāke gina tentin Dawuda da ya rushe. Kufansa zan sāke gina, in kuma mai da shi,
- Ayyukan Manzanni 15:17kusan 51 M.
don ragowar mutane su nemi Ubangiji, kuma duk Al’umman da suke kira bisa sunana, in ji Ubangiji, wanda yake yin waɗannan abubuwa’
- Ayyukan Manzanni 15:18kusan 51 M.
da aka sani tun zamanai.
- Ayyukan Manzanni 15:19kusan 51 M.
“Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Al’ummai waɗanda suke juyowa ga Allah.
- Ayyukan Manzanni 15:20kusan 51 M.
A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini.
- Ayyukan Manzanni 15:21kusan 51 M.
Gama Musa ya yi wa’azi a kowace birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majami’u kowane Asabbaci.”
- Ayyukan Manzanni 15:22kusan 51 M.
Sai manzanni da dattawa, tare da dukan ikkilisiya, suka yanke shawara su zaɓi waɗansu daga cikin mutanensu su kuma aike su zuwa Antiyok tare da Bulus da Barnabas. Sai suka zaɓi Yahuda (wanda ake kira Barsabbas) da kuma Sila, mutum biyu da suke shugabanni cikin ’yan’uwa.
- Ayyukan Manzanni 15:23kusan 51 M.
Tare da su suka aika da wannan wasiƙa. Daga manzanni da dattawa, ’yan’uwanku. Zuwa ga Al’ummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya. Gaisuwa.
- Ayyukan Manzanni 15:24kusan 51 M.
Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna tā da hankalinku ta wurin abin da suka ce.
- Ayyukan Manzanni 15:25kusan 51 M.
Saboda haka dukanmu mun yarda mu zaɓi waɗansu mutane mu kuma aike su wurinku tare da ƙaunatattun abokanmu Barnabas da Bulus
- Ayyukan Manzanni 15:26kusan 51 M.
mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi.
- Ayyukan Manzanni 15:27kusan 51 M.
Saboda haka muna aika Yahuda da Sila don su tabbatar muku da baki abin da muka rubuta.
- Ayyukan Manzanni 15:28kusan 51 M.
Ya gamshe Ruhu Mai Tsarki da mu ma kada a ɗora muku nauyi fiye da na waɗannan abubuwa.
- Ayyukan Manzanni 15:29kusan 51 M.
Ku guji abincin da aka yi wa alloli hadaya, da jini, da naman dabbar da aka murɗe da kuma fasikanci. Za ku kyauta in kun kiyaye waɗannan abubuwa. Ku huta lafiya.
- Ayyukan Manzanni 15:30kusan 51 M.
Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar.
- Ayyukan Manzanni 15:31kusan 51 M.
Mutanen suka karantata suka kuma yi farin ciki saboda saƙonta mai ƙarfafawa.