Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 30–62

The Early Church

Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.

1,007 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Amma wanda Allah ya tā da daga matattu bai ruɓa ba.

  2. “Saboda haka, ’yan’uwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi.

  3. Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba tă iya kuɓutar ba.

  4. Ku lura kada abubuwan da annabawa suka faɗa su faru muku.

  5. “ ‘Ku duba, ku masu ba’a, ku yi mamaki, ku hallaka, gama zan yi wani abu a zamaninku da ba za ku taɓa gaskatawa ba ko da wani ya gaya muku.’”

  6. Bulus da Barnabas suna fita daga majami’ar ke nan, sai mutane suka gayyace su su ƙara yin maganan nan a kan waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci mai zuwa.

  7. Da aka sallami jama’a, Yahudawa da yawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci masu ibada suka bi Bulus da Barnabas, waɗanda suka yi magana musu suka kuma ƙarfafa su su ci gaba a cikin alherin Allah.

  8. A ranar Asabbaci na biye kusan dukan birnin suka taru don su ji maganar Ubangiji.

  9. Sa’ad da Yahudawa suka ga taron mutanen, sai suka cika da kishi suka yi ta munanan maganganu a kan abin da Bulus yake faɗi.

  10. Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagadi, suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Al’ummai.

  11. Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa, “ ‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’”

  12. Sa’ad da Al’ummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata.

  13. Maganar Ubangiji kuwa ta bazu a dukan yankin.

  14. Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka tā da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu.

  15. Saboda haka suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaidar a kansu suka kuwa tafi Ikoniyum.

  16. Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.

  17. A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majami’ar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagadi har Yahudawa da Al’ummai masu yawa suka gaskata.

  18. Amma Yahudawan da suka ƙi ba da gaskata, suka zuga Al’ummai suka sa ɓata tsakaninsu da ’yan’uwa.

  19. Bulus da Barnabas kuwa suka daɗe sosai a can, suna magana gabagadi saboda Ubangiji, wanda kuwa ya tabbatar da saƙon alherinsa ta wurinsa su su aikata ayyuka da alamu masu banmamaki.

  20. Mutanen birnin suka rarrabu, waɗansu suka goyi bayan Yahudawa, waɗansu kuma suka goyi bayan manzannin.

  21. Yahudawa da Al’ummai tare da shugabanninsu suka ƙulla shawara a tsakaninsu, domin su wulaƙanta su su kuma jajjefe su da duwatsu.

  22. Amma suka sami labari suka kuma gudu zuwa biranen Ikoniyum na Listira da Derbe da kuma ƙauyukan kewaye,

  23. inda suka ci gaba da wa’azin labari mai daɗi.

  24. A Listira kuwa akwai wani gurgu zaune a ƙafafunsa, wanda gurgu ne tun haihuwa, kuma bai taɓa tafiya ba.

  25. Ya kasa kunne yayinda Bulus yake magana. Bulus kuma ya kafa masa ido, ya lura cewa yana da bangaskiyar da za tă warkar da shi