- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 13:12kusan 45 M.
Sa’ad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji.
- Ayyukan Manzanni 13:13kusan 45 M.
Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafos a jirgin ruwa zuwa Ferga a Famfiliya inda Yohanna ya bar su ya koma Urushalima.
- Ayyukan Manzanni 13:14kusan 45 M.
Daga Ferga kuwa suka ci gaba zuwa Antiyok na Fisidiya. A ranar Asabbaci sai suka shiga majami’a suka zauna.
- Ayyukan Manzanni 13:15kusan 45 M.
Bayan an yi karatu daga cikin Doka, da kuma Annabawa, sai shugabannin majami’ar suka aika musu suka ce, “’Yan’uwa, in kuna da wani saƙon ƙarfafawa domin jama’a, sai ku yi.”
- Ayyukan Manzanni 13:16kusan 45 M.
Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce, “Mutanen Isra’ila da kuma ku Al’ummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni!
- Ayyukan Manzanni 13:17kusan 45 M.
Allahn mutanen Isra’ila ya zaɓi kakanninmu; ya kuma sa mutanen suka yi bunkasa yayinda suke zama a ƙasar Masar, da iko mai girma ya fitar da su daga ƙasar,
- Ayyukan Manzanni 13:18kusan 45 M.
ya kuma jure da halinsu har shekara arba’in a cikin hamada,
- Ayyukan Manzanni 13:19kusan 45 M.
ya tumɓuke ƙasashe bakwai a Kan’ana ya kuma ba da ƙasarsu gādo ga mutanensa.
- Ayyukan Manzanni 13:20kusan 45 M.
Dukan wannan ya ɗauki kusan shekaru 450. “Bayan wannan, Allah ya ba su alƙalai har zuwa zamanin annabi Sama’ila.
- Ayyukan Manzanni 13:21kusan 45 M.
Sa’an nan mutanen suka nemi a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Shawulu ɗan Kish, na kabilar Benyamin, wanda ya yi mulki shekaru arba’in.
- Ayyukan Manzanni 13:22kusan 45 M.
Bayan an kau da Shawulu, sai ya naɗa Dawuda ya zama sarkinsu. Ya kuma yi shaida game da shi cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake so a zuciyata; shi zai aikata dukan abin da nake so.’
- Ayyukan Manzanni 13:23kusan 45 M.
“Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra’ila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari.
- Ayyukan Manzanni 13:24kusan 45 M.
Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi wa’azin tuba da baftisma ga dukan mutanen Isra’ila.
- Ayyukan Manzanni 13:25kusan 45 M.
Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce, ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. A’a, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’
- Ayyukan Manzanni 13:26kusan 45 M.
“Ya ku ’yan’uwa, ’ya’yan Ibrahim, da ku kuma Al’ummai masu tsoron Allah, a gare mu ne fa aka aiko wannan saƙon ceto.
- Ayyukan Manzanni 13:27kusan 45 M.
Mutanen Urushalima da masu mulkinsu ba su gane da Yesu ba, duk da haka cikin hukunta shi suka cika kalmomin annabawan da ake karantawa kowane Asabbaci.
- Ayyukan Manzanni 13:28kusan 45 M.
Ko da yake ba su same shi da wani dalilin da ya kai ga hukuncin kisa ba, suka roƙi Bilatus yă sa a kashe shi.
- Ayyukan Manzanni 13:29kusan 45 M.
Sa’ad da suka aikata duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka saukar da shi daga itacen suka kuma sa shi a kabari.
- Ayyukan Manzanni 13:30kusan 45 M.
Amma Allah ya tashe shi daga matattu,
- Ayyukan Manzanni 13:31kusan 45 M.
kuma kwanaki da yawa waɗanda suka yi tafiya tare da shi daga Galili zuwa Urushalima suka gan shi. Su ne yanzu shaidu ga mutanenmu.
- Ayyukan Manzanni 13:32kusan 45 M.
“Muna gaya muku labari mai daɗi cewa abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari,
- Ayyukan Manzanni 13:33kusan 45 M.
ya cika mana, mu zuriyarsu, ta wurin tā da Yesu daga matattu. Kamar yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa, “ ‘Kai Ɗana ne, yau na zama Uba a gare ka.’
- Ayyukan Manzanni 13:34kusan 45 M.
Gaskiyar cewa Allah ya tā da shi daga matattu, a kan ba zai taɓa ruɓewa ba, an faɗe shi a cikin waɗannan kalmomi. “ ‘Zan ba ku tsarki da kuma tabbatattun albarkun da na yi wa Dawuda alkawari.’
- Ayyukan Manzanni 13:35kusan 45 M.
Haka kuma aka faɗa a wani wuri. “ ‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’
- Ayyukan Manzanni 13:36kusan 45 M.
“Gama sa’ad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe.