- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 14:10kusan 46 M.
sai ya ɗaga murya ya ce, “Tashi ka tsaya kan ƙafafunka!” Da jin haka, sai mutumin ya yi wuf ya kuma fara tafiya.
- Ayyukan Manzanni 14:11kusan 46 M.
Sa’ad da taron suka ga abin da Bulus ya yi, sai suka ihu da harshen Likayoniyawa, suna cewa, “Alloli sun sauka mana da siffar mutane!”
- Ayyukan Manzanni 14:12kusan 46 M.
Sai suka ba wa Barnabas, sunan Zeyus, Bulus kuma suka kira Hermes domin shi ne shugaban magana.
- Ayyukan Manzanni 14:13kusan 46 M.
Firist na Zeyus, wanda haikalinsa ke bayan birni, ya kawo bijimai da furanni a ƙofofin birni domin shi da taron mutanen sun so su miƙa musu hadayu.
- Ayyukan Manzanni 14:14kusan 46 M.
Amma da manzannin nan Barnabas da Bulus suka ji haka, sai suka yayyage tufafinsu suka ruga cikin taron, suna ihu suna cewa,
- Ayyukan Manzanni 14:15kusan 46 M.
“Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu.
- Ayyukan Manzanni 14:16kusan 46 M.
A zamanin dā, ya bar dukan ƙasashe su yi yadda suka ga dama.
- Ayyukan Manzanni 14:17kusan 46 M.
Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba. Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokutansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.”
- Ayyukan Manzanni 14:18kusan 46 M.
Ko da waɗannan kalmomi ma, da ƙyar suka hana jama’an nan yin musu hadaya.
- Ayyukan Manzanni 14:19kusan 46 M.
Sai waɗansu Yahudawa suka zo daga Antiyok da Ikoniyum suka sha kan taron. Suka jajjefi Bulus da duwatsu suka kuma ja shi bayan birni, suna tsammani ya mutu.
- Ayyukan Manzanni 14:20kusan 46 M.
Amma bayan da almajiran suka taru kewaye da shi, sai ya tashi ya koma cikin birni. Kashegari shi da Barnabas suka tashi zuwa Derbe.
- Ayyukan Manzanni 14:21kusan 46 M.
Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok,
- Ayyukan Manzanni 14:22kusan 46 M.
suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”
- Ayyukan Manzanni 14:23kusan 46 M.
Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da addu’a da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi.
- Ayyukan Manzanni 14:24kusan 46 M.
Bayan sun bi ta Fisidiya, sai suka zo cikin Famfiliya,
- Ayyukan Manzanni 14:25kusan 46 M.
kuma sa’ad da suka yi wa’azi a Ferga, sai suka gangara zuwa Attaliya.
- Ayyukan Manzanni 14:26kusan 46 M.
Daga Attaliya kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antiyok, inda dā aka danƙa su ga alherin Allah saboda aikin da suka kammala yanzu.
- Ayyukan Manzanni 14:27kusan 46 M.
Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Al’ummai.
- Ayyukan Manzanni 14:28kusan 46 M.
Suka kuma jima a can tare da almajirai.
- Ayyukan Manzanni 15:1kusan 51 M.
Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.”
- Ayyukan Manzanni 15:2kusan 51 M.
Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana.
- Ayyukan Manzanni 15:3kusan 51 M.
Ikkilisiya ta raka su suka tafi, yayinda suke ratsawa ta Funisiya da Samariya, suka ba da labari yadda Al’ummai suka tuba. Wannan labarin ya sa dukan ’yan’uwa suka yi murna ƙwarai.
- Ayyukan Manzanni 15:4kusan 51 M.
Sa’ad da suka isa Urushalima, sai ikkilisiya da manzanni da kuma dattawa suka marabce su, sai suka ba su rahoton dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu.
- Ayyukan Manzanni 15:5kusan 51 M.
Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Al’ummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.”
- Ayyukan Manzanni 15:6kusan 51 M.
Sai manzanni da dattawa suka taru don su duba maganar.