- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 12:12kusan 44 M.
Da ya gane haka, sai ya tafi gidan Maryamu uwar Yohanna, wanda ake kuma kira Markus, inda mutane da yawa suka taru suna addu’a.
- Ayyukan Manzanni 12:13kusan 44 M.
Bitrus ya ƙwanƙwasa ƙofar waje, sai wata mai aiki a gidan da ake kira Roda ta zo tă ji ko wane ne.
- Ayyukan Manzanni 12:14kusan 44 M.
Da ta gane muryar Bitrus, ta cika da murna ta gudu ta koma ba tare da ta buɗe ƙofar ba, sai ta koma a guje ta ce da ƙarfi, “Ga Bitrus a bakin ƙofa!”
- Ayyukan Manzanni 12:15kusan 44 M.
Sai suka ce mata, “Kina hauka.” Da ta nace cewa shi ne, sai suka ce, “To, lalle, mala’ikansa ne.”
- Ayyukan Manzanni 12:16kusan 44 M.
Amma Bitrus ya yi ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe ƙofar suka kuma gan shi, sai suka yi mamaki.
- Ayyukan Manzanni 12:17kusan 44 M.
Bitrus ya yi musu alama da hannunsa su yi shiru sai ya bayyana yadda Ubangiji ya fitar da shi daga kurkuku. Ya ce, “Ku gaya wa Yaƙub da kuma ’yan’uwa game da wannan,” sa’an nan ya tashi ya tafi wani wuri.
- Ayyukan Manzanni 12:18kusan 44 M.
Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus.
- Ayyukan Manzanni 12:19kusan 44 M.
Bayan Hiridus ya neme shi bai same shi ba, sai ya tuhumi masu gadin, ya kuma ba da umarni a kashe su. Sa’an nan Hiridus ya tashi daga Yahudiya ya tafi Kaisariya ya kuma yi ’yan kwanaki a can.
- Ayyukan Manzanni 12:20kusan 44 M.
Yana da rashin jituwa da mutanen Taya da na Sidon; sai suka haɗa kai suka nemi ganawa da shi. Bayan suka sami goyon bayan Bilastus, amintaccen bawan sarki, sai suka nemi salama, domin sun dogara ga ƙasar sarkin don samun abincinsu.
- Ayyukan Manzanni 12:21kusan 44 M.
A ranar da aka shirya Hiridus, sanye da kayan sarautarsa, ya zauna a gadon sarautarsa ya kuma ya wa mutanen jawabi.
- Ayyukan Manzanni 12:22kusan 44 M.
Suka tā da murya suka ce, “Wannan muryar wani allah ne, ba ta mutum ba.”
- Ayyukan Manzanni 12:23kusan 44 M.
Nan take, domin Hiridus bai yi wa Allah yabo ba, wani mala’ikan Ubangiji ya buge shi, tsutsotsi kuwa suka cinye shi ya kuma mutu.
- Ayyukan Manzanni 12:24kusan 44 M.
Amma maganar Allah ta ci gaba da ƙaruwa ta kuma bazu.
- Ayyukan Manzanni 12:25kusan 44 M.
Sa’ad da Barnabas da Shawulu suka kammala aikinsu, sai suka komo daga Urushalima, tare da Yohanna, wanda ake kira Markus.
- Ayyukan Manzanni 13:1kusan 45 M.
A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai. Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawulu.
- Ayyukan Manzanni 13:2kusan 45 M.
Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.”
- Ayyukan Manzanni 13:3kusan 45 M.
Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.
- Ayyukan Manzanni 13:4kusan 45 M.
Sai su biyu da Ruhu Mai Tsarki ya aika suka gangara zuwa Selusiya suka shiga jirgin ruwa daga can zuwa Saifurus.
- Ayyukan Manzanni 13:5kusan 45 M.
Da suka isa Salamis, sai suka yi shelar maganar Allah a majami’un Yahudawa. Yohanna yana tare da su a matsayin mai taimakonsu.
- Ayyukan Manzanni 13:6kusan 45 M.
Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani mutumin Yahuda mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu,
- Ayyukan Manzanni 13:7kusan 45 M.
wanda yake ma’aikacin muƙaddas Sergiyus Bulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawulu don yana so ya ji maganar Allah.
- Ayyukan Manzanni 13:8kusan 45 M.
Amma Elimas mai sihirin nan (domin ma’anar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya.
- Ayyukan Manzanni 13:9kusan 45 M.
Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce,
- Ayyukan Manzanni 13:10kusan 45 M.
“Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba?
- Ayyukan Manzanni 13:11kusan 45 M.
Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.” Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora.