Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 30–62

The Early Church

Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.

1,007 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. To, in Allah ya ba su kyauta yadda ya ba mu, mu da muka gaskata da Ubangiji Yesu Kiristi, wane ni da zan yi hamayya da Allah?”

  2. Sa’ad da suka ji haka, ba su ƙara yin faɗa ba, suka kuma ɗaukaka Allah, suna cewa, “To, fa, har Al’ummai ma Allah ya sa suka tuba zuwa rai.”

  3. To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin da ya tashi a kan batun Istifanus suka tafi har Funisiya, Saifurus da kuma Antiyok, suna ba da saƙon ga Yahudawa kaɗai.

  4. Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Hellenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu.

  5. Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji.

  6. Labari wannan abu ya kai kunnuwan ikkilisiya a Urushalima, sai suka aiki Barnabas zuwa Antiyok.

  7. Da ya iso ya kuma ga tabbacin alherin Allah, sai ya yi farin ciki ya kuma ƙarfafa su duka su tsaya da gaskiya cikin Ubangiji da dukan zukatansu.

  8. Mutum ne nagari, cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, mutane masu yawan gaske kuwa suka juya ga Ubangiji.

  9. Sa’an nan Barnabas ya tafi Tarshish don yă nemi Shawulu,

  10. sa’ad da ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antiyok. Ta haka shekara guda cur Barnabas da Shawulu suka yi suna taruwa da ikkilisiya, suka kuma koya wa mutane masu yawan gaske. A Antiyok ne aka fara kiran almajirai da suna Kirista.

  11. A wannan lokaci waɗansu annabawa sun zo Antiyok daga Urushalima.

  12. Ɗaya daga cikinsu mai suna Agabus, ya miƙe tsaye ya yi annabci ta wurin Ruhu cewa za a yi yunwa mai tsanani wadda za tă bazu a dukan duniyar Romawa (Wannan ya faru a zamanin mulkin Kalaudiyus.)

  13. Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga ’yan’uwan da suke zama a Yahudiya.

  14. Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu.

  15. Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu.

  16. Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗan’uwan Yohanna, da takobi.

  17. Sa’ad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bikin Burodi Marar Yisti.

  18. Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa.

  19. Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da addu’a ga Allah dominsa.

  20. A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shari’a, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, daure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa.

  21. Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa.

  22. Sa’an nan mala’ikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Mala’ikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.”

  23. Bitrus ya bi shi suka fita kurkukun, amma bai ma san cewa abin da mala’ikan yake yi tabbatacce ne ba; yana tsammani wahayi yake gani.

  24. Suka wuce masu gadi na fari da na biyu, suka kuma isa ƙofar ƙarfe ta shiga birni. Ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta, suka kuma wuce. Sa’ad da suka yi tafiya tsawon wani titi, nan take mala’ikan ya bar shi.

  25. Sai Bitrus ya dawo hankalinsa ya ce, “Yanzu na sani ba shakka Ubangiji ne ya aiki mala’ikansa yă cece ni daga hannun Hiridus da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”