Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 30–62

The Early Church

Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.

1,007 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana.

  2. Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.

  3. “Yanzu na san cewa ba ko ɗaya daga cikinku wanda na zazzaga ina muku wa’azin mulkin Allah da zai sāke ganina.

  4. Saboda haka, ina muku shela a yau cewa ba ni da alhakin kowa a kaina.

  5. Gama ban yi wata-wata a sanar muku dukan nufin Allah ba.

  6. Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.

  7. Na san cewa bayan na tafi, mugayen kyarketai za su shigo cikinku ba za su kuwa ƙyale garken ba.

  8. Ko cikinku ma mutane za su taso su karkatar da gaskiya don su jawo wa kansu almajirai.

  9. Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye.

  10. “To, yanzu na danƙa ku ga Allah da kuma ga maganar alherinsa, wadda za tă iya gina ku ta kuma ba ku gādo a cikin dukan waɗanda aka tsarkake.

  11. Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba.

  12. Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina.

  13. Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”

  14. Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi addu’a.

  15. Sai dukansu suka yi kuka suka rungume shi, suka kuma yi masa sumba.

  16. Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce, ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa wajen jirgin ruwa.

  17. Bayan muka rabu da su da ƙyar, sai muka shiga jirgin ruwa, muka miƙe zuwa Kos. Kashegari muka tafi Rods daga can kuma muka je Fatara.

  18. Sai muka sami wani jirgin ruwa da zai ƙetare zuwa Funisiya, sai muka shiga muka kama tafiya.

  19. Bayan muka hangi Saifurus muka wuce shi ta kudu, sai muka ci gaba zuwa Suriya. Muka sauka a Taya, inda jirgin ruwanmu zai sauke kayansa.

  20. Da muka sami almajirai a can, sai muka zauna da su kwana bakwai. Ta wurin Ruhu, suka yi ƙoƙari su hana Bulus wucewa zuwa Urushalima.

  21. Amma da lokacin tashinmu ya yi, sai muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu. Dukan almajirai da matansu da ’ya’yansu suka raka mu har bayan birni, a can kuwa a bakin teku muka durƙusa muka yi addu’a.

  22. Bayan mun yi bankwana da juna, sai muka shiga jirgin ruwa, su kuwa suka koma gida.

  23. Muka ci gaba da tafiyarmu daga Taya muka sauka a Tolemayis, inda muka gai da ’yan’uwa muka yi kwana ɗaya tare da su.

  24. Da muka tashi kashegari, sai muka isa Kaisariya muka kuma sauka a gidan Filibus mai bishara, ɗaya daga cikin Bakwai ɗin nan.

  25. Yana da ’ya’ya huɗu ’yan mata da ba su yi aure ba, waɗanda suka yi annabci.