- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 21:35kusan 60 M.
Sa’ad da Bulus ya kai bakin matakala, sai da sojoji suka ɗaga shi sama saboda tsananin haukan taron.
- Ayyukan Manzanni 21:36kusan 60 M.
Taron da suka bi suka dinga kururuwa, suna cewa, “A yi da shi!”
- Ayyukan Manzanni 21:37kusan 60 M.
Da sojoji suka kai gab da shigar da Bulus cikin bariki, sai ya ce wa shugaban ƙungiyar sojan, “Ko ka yarda in yi magana da kai?” Sai ya amsa ya ce, “Ka iya Girik ne?
- Ayyukan Manzanni 21:38kusan 60 M.
Ba kai ba ne mutumin Masar nan da ya haddasa tawaye har ya yi jagorar ’yan ta’ada dubu huɗu zuwa hamada a shekarun baya?”
- Ayyukan Manzanni 21:39kusan 60 M.
Bulus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne, daga Tarshish a Silisiya shahararren birnin nan. In ka yarda bari in yi wa mutane magana.”
- Ayyukan Manzanni 21:40kusan 60 M.
Da ya sami izini daga shugaban ƙungiyar sojan, sai Bulus ya tsaya a matakala, ya ɗaga wa taron hannu. Da dukan suka yi shiru, sai ya ce musu da Arameyanci,
- Ayyukan Manzanni 22:1kusan 60 M.
“’Yan’uwa da iyaye, ku saurari kāriyata yanzu.”
- Ayyukan Manzanni 22:2kusan 60 M.
Da suka ji ya yi musu magana da Arameyik, sai suka yi tsit. Sai Bulus ya ce,
- Ayyukan Manzanni 22:3kusan 60 M.
“Ni mutumin Yahuda ne haifaffen Tarshish na Silisiya, amma a nan birnin ne aka rene ni. Aka horar da ni sosai cikin dokokin kakanninmu a ƙarƙashin Gamaliyel ni ma dā mai himma ne cikin bauta wa Allah kamar yadda kowannenku yake a yau.
- Ayyukan Manzanni 22:4kusan 60 M.
Na tsananta wa masu bin wannan Hanyar har ga mutuwarsu, ina kama maza da mata ina kuma jefa su cikin kurkuku,
- Ayyukan Manzanni 22:5kusan 60 M.
kamar yadda babban firist da dukan Majalisa za su iya shaida. Na ma karɓi wasiƙu daga gare su zuwa ga ’yan’uwansu a Damaskus, na kuma tafi can don in kawo waɗannan mutane a daure zuwa Urushalima don a hukunta su.
- Ayyukan Manzanni 22:6kusan 60 M.
“Wajen tsakar rana da na yi kusa da Damaskus, ba zato ba tsammani sai wani babban haske daga sama ya haskaka kewaye da ni.
- Ayyukan Manzanni 22:7kusan 60 M.
Sai na fāɗi a ƙasa na kuma ji wata murya ta ce mini, ‘Shawulu! Shawulu! Don me kake tsananta mini?’
- Ayyukan Manzanni 22:8kusan 60 M.
“Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ya amsa ya ce, ‘Ni ne Yesu Banazare, wanda kake tsanantawa.’
- Ayyukan Manzanni 22:9kusan 60 M.
Abokan tafiyata suka ga hasken, amma ba su fahimci muryar mai magana da ni ba.
- Ayyukan Manzanni 22:10kusan 60 M.
“Sai na yi tambaya, na ce, ‘Me zan yi, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Tashi, ka tafi cikin Damaskus. A can za a faɗa maka duk abin da aka shirya za ka yi.’
- Ayyukan Manzanni 22:11kusan 60 M.
Abokan tafiyata suka ja ni a hannu zuwa cikin Damaskus, saboda ƙarfin hasken ya makanta ni.
- Ayyukan Manzanni 22:12kusan 60 M.
“Wani mutumin da ake kira Ananiyas ya zo ya gan ni. Shi mai ibada ne wajen kiyaye dokoki wanda dukan Yahudawan da suke zama a can suna girmama shi ƙwarai.
- Ayyukan Manzanni 22:13kusan 60 M.
Ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Ɗan’uwa Shawulu, ka sami ganin garinka!’ A daidai lokacin kuwa na iya ganinsa.
- Ayyukan Manzanni 22:14kusan 60 M.
“Sa’an nan ya ce, ‘Allah na kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa ka kuma ga Mai Adalcin nan ka kuma ji kalmomi daga bakinsa.
- Ayyukan Manzanni 22:15kusan 60 M.
Za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani ka kuma ji.
- Ayyukan Manzanni 22:16kusan 60 M.
Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’
- Ayyukan Manzanni 22:17kusan 60 M.
“Sa’ad da na dawo Urushalima ina cikin addu’a a haikali, sai na ga wahayi
- Ayyukan Manzanni 22:18kusan 60 M.
na ga Ubangiji yana magana. Ya ce mini, ‘Maza! Ka bar Urushalima, gama ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’
- Ayyukan Manzanni 22:19kusan 60 M.
“Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka.